Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani mutum mai suna Fubara Onyengi, da aka caka masa wuka a lokacin da ake takaddama a kan ragowar man fetir da aka yi a ranar sabuwar shekara a Lakeview Phase 2, a yankin Amuwo Odofin a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
Lamarin ya faru ne a unguwar Lakeview Phase 2 dake yankin Amuwo Odofin a jihar.
An kama wani da ake zargi tare da gano wukar da aka yi amfani da shi wajen aikata laifin cikakken bayanin na nan tafe.
Tags:
Labaran Duniya