Malaman Katsina Yarada Rawaninsa !!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Masarautar Katsina ta bayyana dalilin da ya sa Sarkin Katsina ya kori Makaman Katsina Hakimin Bakori kwatakwata daga sarautarsa 


Mai martaba sarkin Katsina Alh. Dr. Abdulmumin Kabir Usman CFR ya sallami Mai girma Makaman Katsina Hakimin Bakori Alh Idris Sule Idris daga bisa sarautarsa kwatakwata.


Za a iya tuna a ranar 23 ga watan Nuwamban 2022 majalisar masarautar Katsina ta fitar da sanarwar dakatar da Hakimin bisa kujerar tasa.


A sanarwar da majalisar masarautar ta Katsina ta sake fitarwa a jiya Alhamis 19 Janairu 2023 kamar yadda Katsina Daily News ta gani, majalisar ta bayyana sallamar Hakimin kwatakwata daga bisa sarautar tasa.


Masarautar ta bayyana dalilin sallamar Hakimin kamar yadda wakilin mai martaba sarkin Katsina, Alh Aminu Nuhu Abdulkadir Ƙauran Katsina Hakimin Rimi ya sa wa hannu


"Bisa ga takardar da majalisar mai martaba Sarkin Katsina Alh DR Abdulmumin Kabir Usman CFR, ta samu daga ofishin Gwamnati mai lamba SEC/54/VOL.VI/1416 ta ranar 18/1/2023, wadda mai girma gwamnan jihar ya tabbatar da korafe-korafe da ya samu, da aka binciko kana da masaniya a kansu, wanda ya kawo rashin zaman lafiya a kasarka.


" Don haka, masarautar Katsina ta yanke shawarar sallamarka daga sarautar Makaman Katsina daga yau Alhamis 19/1/2023


Da fatan Allah Ya bamu lafiya, da zama lafiya amin."

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post