Makarantar Sulaimani(Sulaimani's School of Thought) (1)



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]



An nade Walwala an tura cikin Burgamen Soyayyah, masu Dakonsa sune madawwama cikin Farin ciki da Annushuwa. Itako Takura daure take a saman Turken Kiyayyah. Wasu Mutane ko abubuwan da muke zakewa wajen Sonsu da Kunarsu, ba Ahali ne na wannan Kaunar ba. Rayuwa mai Kyau tana karkashin Lalaben Masoyi na Hakika ne, ba Mazharinsa kawai ba. Duk wani Abu mai Kyau a cikin wannan Duniyar, Wakiline na Soyayyah, Mazhari ne na Kauna. Amma ba shine hakikanin Masoyin ba.


Sirrin Soyayyah shine Zuciya ta hadu da wani wanda ya mallaki Maganadisun iya fahimtarta, tun kafin ta Furta masa Damuwarta ko Farin cikinta. Ya zamo a Tsakaninsu babu bukatar Tarjama ko Dan aike. Soyayyarsa ta zamo Burgame ko Buhu domin Ajiyar Kyawawan Ambato, wadanda sune 'Ya'yan Itacen Soyayyah, ta Gari.


Wannan shine gayar jin dadi, kuma shine manufar kawowa mutane Addini da aiko Annabawa, hakan zai taimaki Mutane su cimma Makurar Walwala, tun a nan Gidan Gwaji dama Gobe Gidan Sakamako.


Me cikin dadin Gidan Al-jannah wanda babushi a gidan Duniya, idan ba zama cikin Mudlaqar Soyayyah da Kauna ba, wadda babu Gillu baHiqdu a cikinta.


To haka ake son Musulmi su zamo a Tsakaninsu, kuma su yadawa sauran Mutane da Sauran Halittu. Masu Jinkai,Tausayi,Rahama, Taimako, da Tallafawa sauran Halittu zuwa ga Kamala.


Amma ina matsalar take? Me ya hana wannan ya tabbata?


Dora Walwala cikin Burgamen Soyayyah ta Jabu, da kauda kai daga kulawar Masoyi na Hakika, shine Dalilin da yasa har yanzu Kunci da Bakin ciki ke mamaye da Rayuwarmu mai cike da Al-hini.


Wannan yasa muna kallon Abubuwa a Birkice kuma a Barkace. Muna mayarda Kafafu a Sama, Kawuna kuma a Kasa. Sai Dimuwa da Shubuha suka rufe mana Idanu.


Zukata suka Danfaru da Soyayyar Karya, suka manta da neman Masoyi na Hakika.

Idan dai samun Masoyi wanda zai iya fahimtar zuciya tun kafin ta Furta mashi Damuwarta shine Sirrin Dadin Soyayyah kuma shine Hutu, to ashe duk wanda zai fi saurin fahimtar ka, ya San bukatunka, tun kafin ka furta masa, shi ne ya kamata a mallakawa Zuciya domin samun Walwala.

Akwai wanda ya San Bukatun Zukata kuma yake fahimtarsu kamar mahallicin zukatan? Akwai wanda ya kamata ka bashi Amanar zuciyarka kamarsa?


To me yasa muke gudun tsarinsa muke rungumar namu tsarin wanda yake cike da Masoyan Bogi?


Kudi, Dukiya, Mata, Gidaje, Mazaje, Sutura, Motoci, Abinci, da sauran su, duk Turaku ne na Kunci idan Ba'a Rinasu da Soyayyah ta Hakika ba, itace Soyayyar Allah. Duk wanda su kadai yake gani, baka iya rabashi da Gaba, Hasada, Karya, Ha'inci, Nifaqa, Annamimanci, Gulma, Keta, da sauran miyagun Dabi'u. Masu tarwatsa Soyayyah. A haka zai kare rayuwa cikin Kunci, domin ya kai walwala inda babu ita.


Duk abunda zuciya ke so, to shi ne zata dinga yiwa biyayyah. Wasu Allah, wasu kuwa Wanin Allah.

Walwala tana karkashin Son Allah da bin Dokokin sa. Takura tana karkashin kama Masoyan Bogi, 'Yan fashin Hanyar Gaskiya

Dan wannan ne General Qasim Sualaimani ya cimma Matsayin da ya cimma, na iya gano Masoyi na Hakika, sai Zuciyarsa ta Rabu da duk wata Soyayyar Bogi, Soyayyar Yaudara. Masoyin Sualimani shine ya mayarda Zuciyar Sualimani ta koma Bankin Jikaqai, Koramar Tausayi, Dutsen Hakuri, Tsaunin Jarumta, Aradun Makiya, Sanyin Idanun Waliyyai.


Wannan ne yasa Sulaimani baya iya zama cikin Iyalanshi, yana jin dadin wasa da Diya da Jikoki, Al-hali akwai wata Jaririya a Hannun ISIS a Syiria ko Iraq wadda take cikin Hadarin rasa Uba ko Kaka. Baya iya ci ya koshi a gidansa Al-hali ga Yamanawa can suna fama da Yunwa. Bayan iya runtsa Idanu ya yi bacci a cikin Iyalai Al-hali ga Marayun Falasdinu can Bani Yahudu na Masu ruwan Azaba cikin tsakiyar Dare. Bayan Sukuni Al-hali raunanan Afghanistan na cikin kangin Sojojin Mamaya.


Da ya ba Allah Amanar Soyayyarshi, sai Allah yasaka Walwalarshi cikin taimakon Mabukata. Ya mayarda Zuciyarshi Mazharin Walwala ta Soyayyar Gaskiya da Wadata. Wannan itace Soyayyah ta Hakika. Idan kana son Sualimani to ka so Allah, sai Allah ya mayarda kai tamkar Sulaimani a cikin Al-umma.


Allah shine masoyin Sulaimani. Zuciyarsa bata san komai ba sai Dakon Soyayyah zuwa ga Bayi. A duk inda ya je Walwala tana nan, Natsuwa tana Sauka.


Darasin Farko a cikin Makarantar Sualimani shine Walwala tana cikin Soyayya da Masoyi na Hakika, ba Masoyan Bogi ba.


Shamsudeen Hassan

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post