— Sheikh Zakzaky (H) a cikin Jawabinsa yanzu haka a wajen Rufe Mu'utamar a garin Katsina.
"Har ma abin al'ajabi cikin maganganun da aka yi kwanan nan dangane da lokacin da aka ga mun yi wani dandali da muka kira shi dandalin Siyasa, wai sai suka ce wannan abin ai da kun yi shi tun farko ma, wai abin da ya faru a Zaria ma da bai faru ba."
"Innalillahi wa Inna Ilaihirraji'un, Wannan manɗiƙin Yazidu ne, kun san Yazidu ne yace ma Imam Zainul-Abideen 'Ya Ali Ma asabakum min musibatin fa bima khasabat aidikum' sai Imam Zainul-Abideen yace 'Ah wannan ayar ba dangane da mu ta sauka ba, wanda ta sauka dangane da mu ita ce 'Ma a saba min musibatin fil ardi wa la fi anfusakum illa fi kitabin min ƙabli an nabra a'a'."
Sheikh Zakzaky a cikin Jawabin nasa ya ƙara da cewa: "Manɗiƙin Yazidu shine ainihin abin da ya sami iyalan Annabi (S) sune suka ja ma kansu, wato kaman sune basu yi biyayya ga hukumar Banu Umayyah ba shi yasa abin da ya same su ya same su. To sai kuma sai Imam Zainul-Abideen yace: "tun ranan gini tun ranan zane, abin da ya same mu dama Allah ya riga ya rubuta zai same mu ne". La muhalata wannan abin zai faru saboda haka ne aka samu ruwayoyi da suka nuna faruwarsa".
"Domin la muhalata su waɗannan mutane baza su bi tafarkin Annabi ba, kuma su kuma Iyalan Annabi baza su bi nasu tafarkin ba. Saboda haka abin da zai faru a Karbala lazim ne ya faru, to haka nan ya faru din. To muma abin da ya faru damu kenan, lazim ne abin da ya faru a Zaria ya faru ɗin saboda mu baza mu taɓa yi biyayyan da su suke da buƙata ba (Ya zama mun daina cewa a bi Allah sai dai a bisu su) to su kuma la muhalatan zasu yi ta yin duk abin da zasu yi suga sun kawar damu".
-