LAILATUL RAGA'IB Kar a sha'afa, gobe ne Alhamis din farko na watan Rajab, akwai sallar da ake yi na kai kuka wajen Allah (T) da neman biyan bukata a wannan ranar ta Alhamis din farkon watan Rajab.




Da farko an so mutum ya azumci yinin Alhamis din.


Sannan bayan Magriba kafin sallar Isha'i, sai ya yi wasu salloli kamar haka;


Raka'a 12 da sallama shida. Wato bayan kowane raka'a biyu zai yi Tashahhud ya yi sallama, sai ya mike ya kawo wata raka'a biyun har ya kammala. 


A kowace raka'a zai karanta: 

- Fatiha 1

- Inna Anzalnahu 3

- Suratul Iklas (Qulhuwa) 12. 


Baya an gama dukkan raka'a 12 din, sai a yi wannan salatin sau 70:


*اللّٰهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ النَّبِيِّ الْاُمِّيِّ وَ عَلَى آلِهِ*


"Allahumma salli ala Muhammadin Nabiyil Ummiyi wa ala alihi."


Sannan sai mutum ya yi sujada yace sau 70 a cikin sujjadar tasa: 


*سُبُّوحٌ قُدُّوسٌ رَبُّ الْمَلائِكَةِ وَ الرُّوح*


"Subbuhul Ƙuddusu Rabbul Mala'ikati War-Ruh."


Sai mutum ya dago kansa daga sujjadar, ya kuma fadin wannan Istigfarin sau 70:


*رَبِّ اغْفِرْ وَ ارْحَمْ وَ تَجَاوَزْ عَمَّا تَعْلَمُ اِنَّكَ اَنْتَ الْعَلِيُّ الْاَعْظَمُ*


"Rabbigfir Warham wa Tajawaz amma Ta'alamu, Innaka Antal Aliyul Azeem."


Sannan sai ka sake komawa zuwa ga sujjadar karshe, ka kuma cewa sau 70:


*سُبُّوحٌ قُدُّوسٌ رَبُّ الْمَلائِكَةِ وَ الرُّوح*


"Subbuhul Ƙuddusu Rabbul Mala'ikati War-Ruh."


Sannan sai mutum ya roki duk bukatunsa a wajen Allah. Insha Allah karbabbiya ce nan take.


— Ana iya duba Mufatihul Jinan babin ayyukan watan Rajab, ko Iƙbal da Biharul Anwar don karin bayani.


Allah Ya sa mu dace.


Sannan Ina rokon yan uwa asani a Addu a Dan Allah

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post