Labari da dumidumin sa 'Yan Sanda a Jahar kano sunci mutuncin yar Jarida, inda su doketa har sai da a kaita asibiti, a halin yanzu tana kwance rai a hannun Allah




zargi Jami’in yan sanda wanda Dco ne a ofishin yan sandan dake Mandawari da Yadda cin zarafin ma'aikaciyar Rahma Radio Naziha Ibrahim a wajen dauko rahoton rikicin ‘yan KAROTA da sojoji Ranar juma'ar da ta gabata a Kano.


Yar Jaridar Naziha ta koka matuka da rashin daukar mataki akan Jami’in, domin ko da yazo duba lafiyarta, saida ya mata kallon rashin da’ah da nuna ko in kula da halin da take ciki, wanda hakan ke nuni da rashin nadamansa akan abinda ya aikata.


Duk da cewa majiyar Dandalin Labarai ta gano cewa kwamishinan yan sandan Jahar ta kano ya bashi umarnin yayi bayani wanda ake kira “query” a turance, hakan baisa Jami’in mai suna DCO Umar Jibril dake Mandawari Division nadamar abinda ya aikata ba. 


Abin jira a gani dai yanzu shi ne mataki na gaba da hukumar yan sanda zata dauka kan wannan Jami’in nata DCO Umar Jibril dake Mandawari Division domin dakile cin zarafi da mutuncin yan jarida da hakan yazama ruwan dare musamman a Jahar Kano karkashin jagorancin CP Dauda Mamman.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post