[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041
Gwamman Babban Bankin Najeriya Godwin Emefeile ya sake jaddada cewa babu gudu babu ja da baya game da wa'adin da babban bankin ƙasar ya saka na daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.
A wani sakon bidiyo da babban bankin ya wallafa a shaifin sa na Tuwita da maraicen ranar Asabar mista mista Emefiele ya ce ya samu rahotonni kiraye-kirayen da jama'a ke yi na buƙatar ƙara wa'adin da bankin ya saka na daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.
Saboda wasu dalilai da suka hadar da rashin samun wadatattun sabbin takardun kuɗin, ko ƙurewar lokaci wajen kai tsoffin takardun kuɗin zuwa bankuna.
Mista Emefiela ya ce ''hakika ina ɗauke da sako maras daɗi ga waɗanda suke tunanin za mu ƙara wa'adin, dan haka ina mai bayar da haƙuri a kan haka, domin kuwa ba abu ne mai yiyuwa b''.
TALLA
''Dalili kuwa shi ne kamar yadda shugaban ƙasa a faɗa har sau biyu cewa kwanaki 100 sun isa duk wanda yake da tsoffin kuɗi da ya je ya musanya su a bankuna'', in ji Emefeile
Ya ƙara da cewa ''mun ɗauki duka matakan da suka dace domin tabbatar da cewa bankuna sun kasance a buɗe domin karɓar tsoffin takardun kuɗi, kuma mun yi imanin cewa kwana 100 sun wadatar a yi hakan''.
Ya ce bankunan ƙasar za su ci gaba da kasancewa a buɗe a ranakun asabar da Lahadi domin sauƙaƙa wa jama'a wahalhalun da suke sha.
Matsayar Shugaba Buhari
Yayin da yake martani game da rahotonni dogayen layukan mutanen da ke shafe sa'o'i domin samun musanya tsoffin kuɗinsu a bankuna, shugaban ƙasar Muhamadu Buhari ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa 'yan ƙasar ba su wahala ba ta fuskar kasuwancinsu, da kuma samun tsaiko wajen musanya tsofiin takardun kuɗinsu da sabbi a yayin da wa'adin da babban bankin ƙasar ya saka ke ƙara ƙaratowa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Mallam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya jaddada cewa an fito da batun sauya fasalin kuɗin ƙasar ne domin yin maganin mutanen da suka ɓoye kuɗin haram, ba don cutar da talaka ba.
Ya kuma ce hakan zai magance matsalar cin hanci da rashawa da ɗaukar nauyin ta'addanci da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa, tare da taimakawa wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito mana.