KOWACE SISTER DA TAKE CIKIN HARKAR NAN YAR SISTERS FORUM CE"------ Malama Zeenatuddeen Ibrahim Zakzaky ......!!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


--Inji Amma Khadija Yusuf a garin Dutsin-ma.


Yayin Da Take jawabinta a wajen tablig ga 'yan uwa sisters a garin Dutsin-ma wanda sisters forum suka shirya a gari,Kamar yadda suke zagayawa a dukkan garuruwan dake zagaye da garin katsina domin isar da saƙon harka.


Wannan satin rundunar tablid din ta sisters forum ta dira ne a garin dutsinma na Jihar inda aka gabatar da Jawabai zuwa ga 'yan uwa sisters da sauran 'yan uwa brazas akan manufar Halittar dan adam da kuma hadafin harka islamiyya sannan kuma akayi magana akan abinda ya shafi tsare-tsaren sisters forum da kuma babban mu'utamar na ƙasa da ƙasa dake tunkaranmu a ranar 27,28 zuwa 29 ga watan junairu na wannan shekaran ta 2023 da muke ciki.


Amma maryam ta gabatar da jawabinta akan manufar halittar ɗan adam, bayan ta kammala ne Amma Fatima ta gabatar da jawabin nata akan hadafin harka islamiyya sannan Amma khadija yusuf ta cigaba da jawabinta akan Tsare-Tsaren sisters forum da ayyukansu sannan tayi magana akan tsare-tsaren mu'utamar da muke tunkara ƙarshen wannan watan, tayi magana ne akan cewa malama zeenah ta tabbatar da cewa:

"Dukkan wata sister da take cikin harkan nan ƙarama ko babba tom 'yar sisters forum ce kai hatta jaririya 'yar sisters forum ce", koda kuwa sister tana cikin wani forum dake cikin harka misali ISMA KO ZAINABIYUN Ds.


A lokacin da take bayani ta bayyana "malam zeenah amatsayin itace wakiliyar sisters forum da take wakiltar dukkan sisters dake cikin wannan harka a bangaren sisters forum kamar yadda a kowane bangarori a wannan harkar suke da wakillai da suke wakilta dandalolinsu ko forum dinsu haka suma sisters forum malama zeenah itace wakiliyar da take wakiltar sisters forum a cikin harka islamiyya baki ɗaya" (Central).


A lokacin da take cikin jawabin ta bayyana cewa

"Adon haka ne ya kasance a wannan lokaci bayan waki'a su malam (h) sun ƙarfafa Samar Da Kyakykyawan tsarin sisters forum daga mataki na (Central) zuwa ƙasa ta yadda zaya kasance suna gabatar da ayyukansu kamar yadda sauran bangarorin harka suke gabatarwa"


A cikin jawabin nata ta Amma Khadija Yusuf ta bayyana yadda Allah ta'ala ya zabi sisters cikin forum din da su malam (h) suka ayyana zasu cigaba da tsara harkokin harka islamiyya a wannan lokaci," tace: hakan ya samu ne ta yadda su sisters forum ya kasance suna ɗaya daga cikin waɗanda su malam (h) su ka yiwa shaida akan suna tuntubarsu a dukkan ayyukansu da suke gabatarwa Lokaci suna tsare a hannun azzalumai, wannan tuntuba da sisters forum keyi shine ya jaza su malam (h) sukayi masu tagomashi su kasance cikin mutanen da zasu riqa tsara al'amurran harka a wannan lokaci da ake ciki na sabon shafi a  harka baki ɗaya" 


Da take jawabi game da mu'utamar ta bayyana irin tsare-tsaren da sisters forum da academic forum keyi domin gabatar da babban mu'utamar na ƙasa da ƙasa wanda zai gudana a garin katsina, anja hankalin 'yan uwa akan muhimmantar da zuwa mu'utamar din domin sayyid zakzaky(h) shine zai zama babban baƘo mai rufe shi mu'utanar din sannan an umarcesu da su Sanar Da shi wannan mu'utanar din ga sauran 'yan uwa,daga bisani akayi tambayoyi aka bayar da amsa sannan akayi addu'a da hotuna aka sallami kowa.


Rahoto

Mazluma D Abdallah


Zakzakiyya Media Team katsina.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post