Ko Kun San Cewa: "Kowanne Mumini Musulmi Ne Amma Kuma Ba Kowanne Musulmi Bane Mumini?.”



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]



-Mumini Shine Wanda Sauran Musulmi Suka Kubuta Daga Harshensa da Kuma Hannunsa.” Wato Baya Cutar da ‘Yan Uwansa Musulmi da Harshensa Misali Yayi Musu Giba Ko Annamimanci Ko Hassada Ko Sharri da Dai Sauransu.”

-Ko Kun San Cewa: "Shi Mumini Ko da Ya Fusata to Fusatarsa Bata Sanya Shi Yayi Abinda Ya Sa6awa Shari’a Ba.

-Ko Kun San? "Bawa Ba Zai Samu Hakikanin Kamalar Imani Ba Har Sai Ya Siffata da Abubuwa Ukku: 

(1)-Ilimi A Fagen Addini. 
(2)-Tsaka-tsaki A Fagen Rayuwa.
(3)-Dauriya Akan Jarabawowi Na Musibu.”

-Ko Kun Cewa: "Mumini Shine Wanda idan Ya Aikata Mummunan Aiki Zai yi Istigfari.”

-Ko Kun San? Yana Daga Cikin Alamomin Fakihi:

-Yin Hakuri.
-ilimi.
-Yawan Yin Shiru.”

-Ko Kun San Duk Wanda Ya Kame Fushinsa to Allah Ta’ala Zai Kame Daga Yi Masa Azaba.”

-Ko Kun San? Imani Shine: Kudurtawa da Zuciya, Furuci da Harshe da Kuma Aiki da Ga6obi. 

-Kun San Cewa: Duk Lokacin Barawo Zaiyi Sata Sai Allah Ta'ala Ya Cire Masa Rigar Imani, Babu Yadda Za'ayi Mai Imani Yayi Sata.

-Kun Kun San Cewa: "Mai Shan Giya ba Zai Sha Giya Ba Lokacin da Yake Shan Giyar Yana da Imani.

-Mai Kisa Ba Zai yi Kisa Ba tare da Hakki Ba Lokacin da Yake Kisan Yana da imani.

-Ko Kun San Cewa: "Duk Wanda Ya Kwatanta Allah Ta’ala da Halittarsa to Yayi Shirka, Duk Kuma Wanda Ya Jingina Masa Abinda Aka Hana A Jingina Masa to Ya Kafirta.

-Ko Kun San Cewa: "Yin Sallah A Farkon Lokaci Yafi Falala, Kuma Ka da Ku yi Sallah A Bayan Fajirin Mutum.

-Ko Kun San Cewa: "Yana Daga Cikin Dabi’oin Annabawa Yin Tsafta da Kuma Sanya Turare.”

-Ko Kun San Cewa: "Ibada ba Itace Yawan Sallah da Azumi Ba, Amma Ibada Itace Yawan Tafakkuri-Tunani- Akan Al’amarin Allah Ta’ala.”

-Ko Kun Cewa: "Allah Ta’ala Yayi Umarni da Sallah da Kuma Bada Zakka to Wanda Yayi Sallah Amma Bai Bada Zakka Ba to Ba Za a Karbi Sallar Shi Ba.

-Ko Kun San Cewa: Duk Wanda Ya Kyautata Zato ga Allah to Allah Yana Nan a Yadda Yake Zatonsa.”

-Ko Kun Cewa: "Duk Wanda Bai Godewa Mutane Kan Wani Abin Alkhairi da aka yi Masa Ba to ba Zai Godewa Allah Ta'ala Ba.”

-Ko Kun San Cewa: Imani Yana da Ginshikai Guda Hudu Sune: 
(1)-Dogara ga Allah.
 (2)-Yarda da Hukuncin Allah.
(3)-Sallamawa ga Al’amarin Allah.
(4)-Fawwala Masa Akan Komai.

-Wassalamu Alaikum.
 Aminu Abubakar

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post