[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
.......Daga lokacin da wata ta shigo miki gida to karki dauka ke bakida wata Power a wurin mijinki sai ita, idan yazo ya nuna miki jiya wance tayi mani kaza Kuma naji dadinsa, idan girki ne ki cire girman kai ki koya koda ba wurinta, idan wani abun ne da bazaki iya ba kuma kiyi kokari ki maye masa gurbinsa da wani abun, kowane lokaci dai ya zama one_one kuke a wurinsa, idan ta fiki acan ke kuma kin fita acan.
Zaman kishi ba hauka bane, kina kuskura kika bi shawarar kawayen banza kika daina yin abinda ya kamata wallahi mijin hannunta zaya koma, ke ki tashi a tutar babu, karshe kiji yana cewa zaman yaranki kikeyi da tuni ya sake ki.
Competition a keyi a wurin kula da miji, shiyasa akeso tun kina ke daya ki saba da hakan ba wai sai kinji za'a kawo miki wata ba sannan ki rude ki fara gyara, abinda bakiyi shekaru kaza da suka wuce ba shine zaki ara ki yafa a rana daya, kuma kike so aga kinyi daidai dashi, gaskiya da kamar wuya.
Kai ma kuma mai gida sai a rika kokarin yin adalci, idan kaga wani abu wanda kake so uwar gida tayi maka wanda ada bata yi cikin hikima zaka sanar da ita, ba gatsau zaka fada mata ba, zataga kamar dan ka karo aure yasa ka fara ci mata fuska, haka karka kuskura ka rika yabon wata a gaban wata, duk yanda ta nuna maka ba komi wallahi sai taji ba dadi kazo kana yaba mata wata ba ita ba, domin raina kokarin ta ne kakeyi idan kana mata haka, ke kuma duk sanda yazo miki da korafi a kanta ko yana yaba miki ita karki zake da yawa kiyita kushenta idan haka yake ko kiyita bata rai idan yabonta yake, yana kawo miki korafi kice dashi hakuri akeyi ki kauda zancen, idan yana yabonta ma ki nuna kinji dadi ki kauda zancen karki bari firar tayi tsayi. Sannan karki yarda yana dauko maganganunta yana kawo miki.....
zan cigaba insha Allah
Allah ya anfanar damu 🤲🏼
✍🏽 Zarah A Zamsarf 🍂✨