Kira Ga Yan As'habul Kahafi Kuyi Koyi Da Almajiran Sayyid Zakzay(h).....!!!




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Shugaba shine babban jagora wajen kawo dukkan wani cigaba ko ci baya cikin kowacce irin tafiya, idan aka sami jagora tsayayye jajurtacce akan tafiya za aga cigaba da kuma dorewar wannan tafiya. 


Amma a duk inda aka sami jagora rarrauna ko mai kwadayi ko kuma mai yin jagorancin nasa bisa wata manufa ta qashin kansa, to, akwai naqasu cikin wannan tafiya. Domin in makwadaici ne zai zama wasu ne zasu riqa juya shi, shi kuma ya riqa juya ku ta fuskar wadanda ke juya shi. Shi kuwa rarrauna zai iya fasa yin abinda yake yi musamman in ya sami barazana daga mahukunta ko taron dangin wasu jama'a. 


Sheikh Abdul-Jabbar (H) jagora ne tsayayye abin koyi, kuma abin alfahari ga dukkan mabiyansa. Za mu iya fahintar haka idan muka kalli dakewarsa kan wannan jarraba da Allah ya jarrabce shi da ita irin wacce yake yiwa manyan bayinSa Manzanni (A. S). 


Yayin da kafirai suka dira kan Annabi (S. A. W. W) a yaqin Uhud da nufin kawo qarshensa daidai lokacin da Sahabbai suka gudu suka bar shi, sai wasu tsiraru da basu wuce mutane takwas (8) ba suka bashi kariya, duk sara da sukan da ake kawowa sai ta tsaya a kansu, har Allah ya kawo nasararSa gare su.


Idan muka kalli waqi'ar Zaria wacce ta auku cikin shekarar 2015, jami'an tsaro/tsoro basu iya kaiwa ga jagoran 'yan Shi'ah ba har sai da aka qarar dasu, wanda hakan ke nuna tsantsar sallama bisa yarda da abinda yake jagorantarsu a kansa. Sai hakan ya nuna cewa aiki ne suka yi a akace irin aikin Sahabban Annabi (S. A. W. W) na gargaru masu sadaukar da rayukansu don bada kariya ga jagora. 


A lokacin da jagoransu ke hannun azzalumai sun riqa amfani da kudadensu ta kowacce irin hanya wajen bayyanarwa duniya wannan zalunci da ake yiwa jagoransu da ma su almajiran nasa. 


Bayan sadaukar da rayukansu, mutum na iya zare a qalla dubu goma (#10,000) ya tafi Abuja (center) na azzalumai don nuna musu rashin amincewa da cigaban zaluncin da suke yi, kuma mutum ya shafe kwanaki ko wata ba tare da ya dawo gida ba. 


Yayin da ake shari'a kuwa, akwai masu bayar da sama da miliyan, wasu dubban daruruwa, wasu kuma dai gwargwadon halin da suke dashi. Sadaukarwa ta kowacce fuska, kuma a qarshe Allah ya basu nasara.


Na'am, na san ba wai komai ya qare bane, domin sunnar Allah ba ta canzawa. A duk lokacin da azzalumai su kaga gazawarsu za su qara fitowa ta wata hanya, sai a qarshe dai hanyar tasu za ta qure. 


Na san a taqaice almajiran Sheikh Abdul-Jabbar (H) ba za su gaza miliyan ba, da ace kowanne daga cikinsu zai zare naira dari (#100) daga abinda Allah ya hore masa domin wannan shari'ar, da za a samar da miliyan dari (#100,000,000), kuma na san za a iya samun masu bada #500, #1,000, da ma sama da haka. Matsalar dai ita ce rashin sadaukarwa. 


Na san kuwa matuqar za ayi haka, tabbas za a sami wasu masu bada gudumowa wadanda ba almajiransa bane, sai dai ace magoya bayan gaskiya da qin zalunci. 


Na ga wasu sunyi wannan tunani har ma sun fitar da account number wacce za ayi amfani da ita wajen wannan tallafawa.


Nima kuma sai naga ya kamata na taimaka wajen bayyanawa almajiran nasa muhimmancin wannan aiki da fa'idar da za a samu matuqar anyi wannan sadaukarwa. 


Shine na bada misali da almajiran Sayyid Zakzaky (H), domin sun kai a bada misali dasu wajen sadaukar da Rayuka da dukiya. 


YAA ALLAH KA BADA KARIYA GA SHEIKH ABDUL-JABBAR (H) TARE DA KUNYATA DUKKAN WANI AZZALUMI DA MUNAFUKI .


🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Daga wakilanmu na Bauchi. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


15th January, 2023/ 23rd Jimada-Sani, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post