[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
hankali kamar littafi yake shi kuma ilmi kamar rubutun da yake cikin littafin ne! rubutu baya CIN Sunan sa rubutu, in ba a jikin allo ko takarda ba! Haka kuma allo ko takarda basa zama littafi sai da rubutu! Wannan ya nuna ilmi da hankali ba Abu daya bane,
Da yawan malamai suna kallon su ne a matsayin abubuwa guda biyu inseparable Amma Imam Ali shine wanda ya sharhanci ilmi da hankali ya Raba su, kamar yadda Jikan sa Imam ja'afar al sadeeq ya zama mutum na farko da ya Raba Philosophy da science,
ILMIN TAFIN HANNU!
Ilmi ne da yake sauka daga Qudirar Allah, kasancewar babu wani Abu da Allah ya halita wanda ba shi da dalili, haka yake har Akan zanen tafin hannu, shi albishir ne na wasu bayanin abun da yake tattare da Dan Adam da Allah zai wanzar Akan sa!
, Qudirar mutum a jikin tafi daya an rubuta Abinda aka haife shi da shi na dabi'ah ko kwayar halitta tsawon rai ko akasin hakan, , sannan kuma Abinda zai samu a duniya wanda addu'ah zata juya su yana dayan tafin hannun , sai dai akwai banbancin tsakanin maza da Mata, misali,
QADDARAR MATA tana hannun dama wacce bata sauyawa , a Yayin da saqonnin sauyin rayuwar ta wato albishir zai dinga zuwa Mata a hannun ta na dama!
QADDARAR maza kuma tana hannun hagun su, albishir din su yana zuwa ne a hannun su na dama,
Wannan ba yana nufin wanda ba shi da hannu guda daya ko duka biyun ba shi da QADDARAR bane, a'a shi ya rasa littafin karanta tasa qaddarar ne kawai, domin albishir din da zai zo masa babu damar kar6ar saqon,
Shi ilmi ne da ba'a karanta shi da idanu sai da kwakwalwa, Don haka yake da matuqar wahala! Sannan ba wai haqiqa duk Abinda ya ke a cikin ilmin 100% yake tabbatuwa ba! Sai dai Dan Adam bai isa ya gujewa Qaddarar sa ba!
RABE RABEN HANNUWA! a cikin dabi'ah sune
1) Akwai masu dogon tafi da dogon yatsu,
2) masu guntun tafin hannu da guntayen yatsu,
3) masu guntun tafi da dogon yatsu
4) masu dogon tafi da guntun yatsu,
Duk duniya kowa yana cikin wadannan rukunin ne Guda hudu, sune ake cewa TURABI, NARI, HAWA'I da kuma MA'I,
sune masu tafin hannu ja da fari da baqi da kuma Mai dabbara dabbara, yakamata in sanar da ku wanne rukuni ne Nari ko turabi da sauran su domin cikin sauqi Ka fahimci rukunin da kake , Amma kasancewa babu ishashshen lokaci sai mu tara a rubutu na gaba!