Harkar Islamiyyah !!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


 Tafiyace ta Kamala, hanya ce ta samun babban Rabo, wanda babu irinsa. Gida ne na neman shiga zurin Bayi Nagartattu. A haka Madugunta ya Tsara ta, domin ta yi Mashabaha da Tafarkin Manzanni da Waliyyai. 


Ba cewa ake duk wanda bai cikinta Batacce ne ba, ko Halakakke, Sam ba haka bane.


 Illa dai ya tanadi Amsarda zai bawa Allah gobe, idan Ya Tambayeshi me hanashi biyayya ga Dokokin shi, me ya hanashi motsi wajen ganin Addinin Allah ya yi iko da doron Kasa. 


Ita wannan hanyar neman Uzuri ne a wajen Allah, idan irin wannan Tambayar ta bijirowa Mutum gobe Qiyama. 


A gurin masu ita, duk Musulmi sunansa Musulmi. Illa dai kawai ya tabbatar hanayar da yake a kai, yana da Hujjar binta, faqat. Babu halakakke sai wanda yaki bin koyarwar da yayi Imani cewa itace dai-dai. Domin hakan dai-dai yake da yanka Wuyansa da kansa. 


Ba kungiya bace Fikira ce, balle ta Kafirtar, ko Ta Batar, ko ta Zindikantar, ko ta Mushrikantar. 


Imani ce da aikin Kirki. Gwadabe ce zuwa ga samun Dacewa. Yasoso ne izuwa ga Gafarar Allah da Rahamarsa. 


Idan kaga Dan Harka na kallon wani a matsayin Batacce ko Dan Wuta, to daga lokacin ya mayarda ita harka Firqa ta Aqida kenan, ko Kungiya ko Mazhaba. Wannan ko raba Gari ne da Fikirar Harka Islamiyyah. 


Ita Uwa ce mai Jinkan Diyanta, Mahadace mai Saukake Tafiya, Girgije ce mai Kyauta da Ruwan Rahama, Korama ce Mai kosarda Dabbobi, Tsuntsaye da Mutane.


An Tsarata ne bisa Mahangar cewa duk Mutum Mai Daraja ne, koma minene Addininshi. Hatta ma wanda bayada Addini. Yanada Al-farmarsa ta zamansa Mutum.


To balle Musulmi, balle, balle, balle Dan Harka Islamiyyah.


Ba'a kora, sai dai Mutum ya kori Kansa. Biyayya ake bisa Irshadin Malami da Dalibansa, Shehi da Muridansa, Jagora da Mabiyansa.


Babu wanda yafi wani a cikinta, sai wanda yafi dagiya wajen bin Allah fakat.


Shamsudeen Hassan

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post