Harda 'Yan Izala/Salafiyya A Cikin Masu Fahimtar Maulana Sheikh Dr Abduljabbar Nasiru Kabara !!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


✍️ Saifullahi Murtala Jibia.


Wato wannan babban Malamin da kuke iya gani tare da Malam a jikin hotuna. Na ga wani jawabi na shi, a lokacin da ya ziyarci Dr Sheikh Abduljabbar (H) a ɗakin karatunsa ( Baharul aɗlass library ) sai da na kusa in zubar da hawaye 😭😭 !!!


GA KAƊAN DAGA KALAMAN SA :

________________________________


" Tsakani na har ga Allah ,ni a tarihin rayuwata Allah shi gafarta malam.Ban taba ganin malami ba kamarka .Ni Ɗan'izala ne cikakke. Izala ita ta haife ni. Wanda ya haifi Mahaifina shi ne sakataren Izala na farko a tarihin Nigeria ,

Mahaifi na shi ne sakataren Jama'atu Izalatul Bidi'a na Katsina baki ɗaya. Amma Allah gafarta Malam, kawai a vidio wata rana na tsaya na saurari karatunka nasan yadda kake faɗin gaskiya, inda yau a ce Abubakar Gumi (R) na da rai , wallahi tallahi, abin da kake yi shi zai cigaba da yi." KASH !!! ANAN VIDION NAWA YAKE ƘAREWA.


TO JAMA'A BA KWA GANIN DUK WANDA AKA HANA SHI YA SAURARI KARATUN MALAM ABDULJABBAR (H) BA A ƘWARE SHI BA ???????


👂ZA KU YI SHARA'A GABAN ALLAH DA MALAM, YA YIN DA KA JI JITA-JITA A KAN SA KUMA KA CIGABA DA YAƊA TA , ALHALI BA KA JI DA KUNNUWANKA BA 👂👂👂👂👂 !!!!


👉 Annabi (saw) da ya fi ƙarfin Kafurai a hujja, sai suka ce kada a saurare shi, a rinƙa tayar da hayaniya idan yana karatu . ƘUR'ANI YA BA MU LABARI :👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


وقال الذين كفروا لا تسمعوا لهذا القرءان والغو فيه لعلكم تغلبون. , (( سورة فصلت 26))


Ya Allah Ka nuna mana gaskiya, kuma Ka ba mu ikon karɓa a duk inda muka gan ta ko da ba a cikin ƙungiyar mu ba ne, kuma Ka nuna mana ƙarya, Ka ba mu ikon guje ma ta ko da a cikin ƙungiyar mu ne 🙏. 


📢 INA TARE DA DR. ABDULJABBAR NASIRU KABARA KANO %%%%%%%%%. 


🇳🇬 AS'HABULKAHFI JIBIA SOCIAL MEDIA TEAM 11/01/2023 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post