Hadafin Harka Da Burin Tabbatar da Addinin Muslumci....!!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 



Daga Saifullahi M. Kabir


Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha fada cewa Harkar Musulunci tana da abin da ake kira ‘Principle’ akwai kuma ‘Policy’.


Principle; shine hadafin da Harka ta doru a kansa. Wato manufar Harkar, wanda shi har abada ba zai taba canzawa ba. Duk lokacin da aka wayi gari an canza Principle to ba Harkar Musulunci ake yi ba kenan, saboda an sauka daga hadafi an koma wani abu daban.


Babban hadafin Harka shine neman uzuri a wajen Allah (T) ta hanyar cewa mun tashi a matsayin ‘ya’yan Musulmi, mun tsinci kanmu a wata al’umma da ke amsa sunan Musulunci, amma ba musulunci ke iko da rayuwarsu ba, alhali in da sun so addinin ya yi iko da rayuwarsu da baa bin da zai hana su iyawa. Amma suka zabi su cigaba da zama karkashin wani tsari na kafirci da danniya, wanda aka kafa shi bayan an rusa tsarin Allah, an shekar da jinanen bayin Allah.


Sai Allah (T) ya haskawa mai kira hadarin hakan, sai ya tashi ya bayyana tawayensa ga wannan tsarin da masu tafiyar da shi, ya kuma jaddada mika wuyarsa ga Allah (T) akan zai bi addininsa. Sannan bai tsaya haka kawai ba, ya kira yi mutane akan su zo a yi wannan tawaye ga tsarin kafirci din, a yi kokarin tabbatar da tsarin Allah tare da su. Hadafinsa da wadanda suke tare da shi shine, kiran al’umma zuwa ga kokarin tabbatar da ikon addinin Musulunci a rayuwar dai-daiku, da kuma in yanayi ya bada ya zama a al’umma baki daya.


Tabbatar addini a doron kasa na bukatar amsawar jama’a, ko da yake ba sai masu yawa ba, amma amsawar masu yawa din na nufin sun fahimci abin da ake son ya wanzu ne, kuma da fahimtarsu ne kawai zai yiwu a yi shari’ar Allah (T) a gare su. Don haka Shaikh Zakzaky ya sha fada tun shekaru 40 baya har zuwa yau din nan, cewa abin ba yana hannunmu bane, yana hannun Allah (T) ne. Ya kan ce, namu kawai shine mu yi kira, amsawar mutane daga Allah (T) ne, in ya so sai ya kimsa musu su fahimta.


Idan Allah bai nufi mutane sun fahimta sun zo an yi da su ba, har duk muka yi Shahada, ko ajali ya riske mu muna wannan kiran, muna fatan ya zama muna da uzuri a wajen Allah (T), a yayin da za mu ce masa, Ya Ubangijinmu, mun kira al’ummar a ta fandare daga bin dokokinta a rayuwarta na daidaiku da jimlarta, mun yi kokarin su zo mu hadu mu tai da dokokin, amma sun ki amsawa, manyansu sun dira mana da hantara, kamu, harbi da kisa da dukkan nau’in cutarwa. Amawan al’ummar suna yaba musu a kan cutarwar da suke mana. amma mun yi kokarin aikata addinin da shari’arka a gwargwadon mustawar iyawarmu. Ya Allah ka karbi uzurinmu, hakika ba mu kasance masu Imani da wani tsari da ya sabawa littafinka da addinin da ka aiko Annabinka (S) da shi ba.


Ta yiwu kace ai kuma din ba addini kuke aiwatarwa 100% a tsakaninku ba. Sai nace maka, akalla muna kamantawa, kuma ko ba komai wannan ne dalilin da ya sa Jagora, kullum kan tunatar da yan uwa cewa mafi girman gudummawar da kowanensu zai ba Harka din shine ya gyara kansa. Ya kan ce ‘Ka gyara kanka a farko, domin in b aka gyaru ba ba zai taba yiwuwa ka gyara waninka ba.’ Kuma a lokuta daban-daban ya sha tunatar da mu cewa gobe kiyama Allah (T) zai wa kowane mutum hisabi shi kadai ne daga shi sai Allah (T), don haka kowa ya gyara kansa ko don wannan tsayuwar, ka san me z aka gabatarwa Allah (T).


Wannan har abada shine hadafin Harkar Musulunci, kira ne zuwa ga komawa tsarin Allah (T), mutane baki daya su amsa, ko kuma kadan su amsa, ko kuma ya zama ba wanda suka amsa kiran, shi mai kiran ya yi nasara. Kamar yadda da yawa akwai Annabawan da Allah (T) ya aiko, suka yi kira zuwa ga mutane, hadafinsu shine a bi Allah (T) a kangarewa tsarin da ya saba masa, amma sai al’ummunsu suka ki amsa musu, sai kadan. Wasu ma sam ba su samu wanda suka amsa din ba, bare su yi yawa, bare su kafa gwamnatin Allah (T), har suka koma ga Allah suna masu kira ne, alhali mutane sun wanzu a bin gwamnatin Shaidan tsinanne.


Su kuwa Annabawan da aka ki amsa da'awarsu aka tsangwame su har aka kashe su, sun yi nasara ko ba su yi ba?


Zan cigaba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post