Gudunmawar Shaheed Qaseem Sulaymany ga Al'ummar Musulmi da Duniya baki ɗaya....!!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 



Shaheed Qaseem Sulaymany, an haifeshi a 11 ga watan March a shekarar 1957, kuma yayi shahada a 3 ga January 2020 yana da shekaru 62.


Shaheed Qaseem Sulaymany ya tashi a zuriyya talakawa (Masu karamin karfi), kuma ya kasance yana aikin karfi don biyawa ahalinsa basussukan da ake binsu lokacin da yake samarta, bayan juyin juya halin ƙasar Iran ya jona IRGC a 1978-79 lokacin yana Matashi.


Ya halarci yaƙin da akayi na Iran-Iraq a shekarar 1980-1988, tun fara yaƙin har karshen sa. Sannan ya samu muƙamin Birgediya Janar wanda ya jagoranci rundunar da take kula da iyakar Iran ta kudancin ƙasar domin yaƙi da masu safarar miyagun ƙwayoyi.


A lokacin Yaƙin Taliban a 1990 ya zama mai kula da dukkan tsaron ƙasar Iran, a 1998 ya zama kwamandan Rundunar Quds Force.


A karkashin Jagorancinsa da yayi na Quds Force ya taka muhimmiyar rawa wajen hana mamayar Ƴan Ta'adda a ƙasashen Labanon, Iraq da Syria, kuma yana cikin mutanen da suka assasa Ƙungiyar Hezbollah a Lebanon kuma yake sanya ido wajen gudanar da ayyukan kungiyar.


Sannan ya bayar da muhimmiyar gudummawa wajen Kafa kungiyar Hamas da Islamic Jihad a Palestinu, sannan ya takawa Amurka burki na kokarin mamaye Iraq a shekarar 2003, a 2011 ya zama Major General.


Shaheed Qaseem Sulaymany ya karar da dukkan rayuwar wajen kariya da hidimtawa al'umma, har zuwa lokacin da Amurka ta yi amfani da Jirgi marar matuki suka Shahadantar dashi.


Amincin Allah ya tabbata a gareshi a ranar da aka kashe shi da kuma Ranar da zai tashi a matsayin Shahidi, Mazlumi.


Jafar Bala Jr.

2/1/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post