Game Da Azumin Tsofaffi (Siyamu Rajab) !!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Aliyu Samba.


Jiya na zo shige wa ta wani masallacin juma'a a Unguwar mu sai na ci karo da mai jawabin (pre kutbah) yana batu akan watan Rajab, yake cewa daga bidi'o'in da ake gudanarwa a wannan watan akwai wani azumi da ake cewa azumin tsofaffi, ya ce bai da asali a addini kuma Annabi bai yi ba, bai kuma yi umarni da ayi ba. Na shige kawai ina murmushi, domin bana mamakin wannan kalmomi daga bakin dan salafiyya, maadaama aka ce ibada ce da zata kusanta bawa da ubangiji, zasuyi iya yinsu su yake ta musamman idan suka ga sufaye da yan Shia suna dabbaƙawa, shiyasa basa zikiri, da maulidi, a wajensu duka bidia ne.


Madogarar masu inkarin wannan azumi na Rajab itace hadisi kamar haka :


ﺣَﺪَّﺛَﻨَﺎ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢُ ﺑْﻦُ ﺍﻟْﻤُﻨْﺬِﺭِ ﺍﻟْﺤِﺰَﺍﻣِﻲُّ، ﺣَﺪَّﺛَﻨَﺎ ﺩَﺍﻭُﺩُ ﺑْﻦُ ﻋَﻄَﺎﺀٍ،

ﺣَﺪَّﺛَﻨِﻲ ﺯَﻳْﺪُ ﺑْﻦُ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟْﺤَﻤِﻴﺪِ ﺑْﻦِ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِ ﺑْﻦِ ﺯَﻳْﺪِ ﺑْﻦِ

ﺍﻟْﺨَﻄَّﺎﺏِ، ﻋَﻦْ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥَ، ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻴﻪِ، ﻋَﻦِ ﺍﺑْﻦِ ﻋَﺒَّﺎﺱٍ، ﺃَﻥَّ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲَّ ـ

ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ـ ﻧَﻬَﻰ ﻋَﻦْ ﺻِﻴَﺎﻡِ ﺭَﺟَﺐٍ .

Daga ibn abbas yace: Manzon Allah SAWA ya hana a azumci watan Rajab.

Duba Sunan Ibn Majah,Hadisi na 1743


Wannan hadisi ne da'ifi absa qa'idar Ahlussunnah domin a isnadin akwai:

ﺩَﺍﻭُﺩُ ﺑْﻦُ ﻋَﻄَﺎﺀٍ

Wanda abinda manyan maluma suka hadu akai akan sa shine ba a karɓar hadisan sa. Shiyasa ma Bukhari yace:  ، ﻣُﻨْﻜَﺮُ ﺍﻟْﺤَﺪِﻳﺚِ

Daraqutni yace:ﺩَﺍﻭُﺩُ ﺑْﻦُ ﻋَﻄَﺎﺀٍﻣﻦ ﺃﻫﻞ ﻣﻜﺔ ﻣﺘﺮﻭﻙ


Duba Lisanul Mizan Na Asqalani,Tarjama 3039


Wannan ya sanya kai tsaye za ace wannan hadisi da'ifi ne kuma ba a hujja da shi a bisa ka'idar makarantar Ahlussunnah.


Watan Rajab wata ne mai tarin albarka, domin yana daga watannin da Annabi yayi addua ta musamman akan su, kamar yadda yazo a hadisi kamar haka:

ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ، ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﺒﻴﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ ، ﻋﻦ ﺯﺍﺋﺪﺓ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ

ﺍﻟﺮﻗﺎﺩ ، ﻋﻦ ﺯﻳﺎﺩ ﺍﻟﻨﻤﻴﺮﻱ ، ﻋﻦ ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﻗﺎﻝ : ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ

ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺇﺫﺍ ﺩﺧﻞ ﺭﺟﺐ ﻗﺎﻝ : ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻨﺎ ﻓﻲ

ﺭﺟﺐ ﻭﺷﻌﺒﺎﻥ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻟﻨﺎ ﻓﻲ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﻭﻛﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ : ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ

ﻏﺮﺍﺀ ﻭﻳﻮﻣﻬﺎ ﺃﺯﻫﺮ .

Allah kayi mana albarka a watan Rajab, da Sha'aban da Ramadan........ 


Duba Musnad Na Imam Ahmad,1/259


Wannan hadisi ya nuna mana girman watan Rajab da kuma girman ibada a cikinsa, domin wata ne mai albarka da kowanne mumini zai fatan samun wannan albarkar, daga hanyoyin samun albarkar sa kuwa akwai ibada, daga mafi soyuwar ibada wajen Allah akwai azumi.


Duk da nasan wasu zasu iya inkarin hadisin da cewa ai a isnadin akwai  ﺯﺍﺋﺪﺓ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺮﻗﺎﺩ da kuma  ﺯﻳﺎﺩ ﺍﻟﻨﻤﻴﺮﻱ, zasu iya cewa ai Za'idatu Bin Abir Riqaad Matruki ne, wanda a hakika amintacce ne saboda dalili kamar haka.


Umar Al Qawariri (Malamin Bukhari) yace:

 ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﺑﻪ ﺑﺎﺱ ﻭﻛﺘﺒﺖ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻋﻨﺪﻩ

*(Tahzibul Kamal Na Mizzi,3/258)


Khalid Bin Khadash(Almajirin Muslim Bin Qutaiba) yace:

ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺯﺍﺋﺪﺓ ﺍﻭ ﻣﻌﺎﺫ ﺻﺪﻭﻕ ﻛﺎﻥ ﻟﺤﻤﺎﺩ ﺑﻦ ﺯﻳﺪ

Yahya Bin Ma'in yace: ﻻﺑﺎﺱ ﺑﻪ

Bazzar yace: ﻻﺑﺎﺱ ﺑﻪ


Akan rawi na 2 da suke suka mai suna ﺯﻳﺎﺩ ﺍﻟﻨﻤﻴﺮﻱ

Shima ga shedar da ya samu nan daga shuwagabbannin fannin jarhi da ta'adilin Ahlussunnah


Yahya Bin Ma'in yace: ﻻﺑﺎﺱ ﺑﻪ

Ibn Adiyy yace: ﻋﻨﺪﻱ ﺍﺫﺍ ﺭﻭﻱ ﻋﻨﻪ ﺛﻘﺔ ﻓﻼ ﺑﺎﺱ ﺑﺤﺪﻳﺜﻪ


Banda abin ustazai ma, wai shin sun manta yadda azumi yake da falala, har aka ruwaito yadda Annabi yake yawaita shi bama a watan Rajab ba kawai? Mu koma mu ga


ﻋﻦ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﺑﻦ ﺣﻜﻴﻢ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭﻱ - ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ - ﻗﺎﻝ : ﺳﺄﻟﺖ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﺒﻴﺮ ﻋﻦ ﺻﻮﻡ ﺭﺟﺐ، ﻭﻧﺤﻦ ﻳﻮﻣﺌﺬ ﻓﻲ ﺭﺟﺐ، ﻓﻘﺎﻝ : ﺳﻤﻌﺖ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ - ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ- ﻳﻘﻮﻝ : « ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - ﻳﺼﻮﻡ ﺣﺘﻰ ﻧﻘﻮﻝ ﻻ ﻳﻔﻄﺮ، ﻭﻳﻔﻄﺮ ﺣﺘﻰ ﻧﻘﻮﻝ ﻻ ﻳﺼﻮﻡ. 

Idan ba zakuyi ibada ba kada ku hana masu yi don Allah. Ga wanda yake da niyya yayi azumin sa kuma zai samu lada da daukakar daraja a wajen Allah. Wanda yaga bai iyawa ba lallai ba dole, addini dan sauki ne. Allah ya datar damu.


Repost

©Aliyu Samba

13022021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post