Ga Sako Nan In Za ka bi Ka bi......!!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 

 

Wato a taqaice abin da nake cewa, ‘destiny’ xin al’ummar nan yana hannunmu ne, kuma ba zai tava yiwuwa kana tunanin wai gyaran Allah kawai a wayi gari a ga an gyaru ba.


Gyaran Allah shi ne me kake so Allah ya yi maka? Ya aiko da wane Annabi? Ya riga ya aiko. Ko ya sauqar da wane Alqur’ani? Ya riga ya sauqar. 


Ba abin da zai yi maka illa ga saqon nan, in za ka bi ka bi, in ba za ka bi ba kuma ya rage maka, a haxu a ranar hisabi. 


To, ni yanzu na ga kamar mutane sun yi saranda ga halin da suka sami kansu ne, ana jiran kawai a yi ta tafiya haka nan.


Kuma kullum abubuwa sai qara tavarvarewa suke yi da lalacewa. 


𝐈n ka ga wannan nau’in lalacewa ya fito, sai ka ga na kashegari ya fi shi muni. 


Sai ka ga wani ya sake kunno kai, shi kuma ya fi na jiya, kuma haka ake ta tafiya ana dai zaune haka nan kawai. 


Abin da nake cewa in waxansu mutane in za su zama ma’azurai, musulmi ba shi da uzuri, don shi tsiransa nahannunsa. Shi Allah Ta’alaya fifita da shiriya, sai ya ajiye waje guda. 


Ba wata mafita gare mu illa mu san cewa mune da kanmu za mu yi, ba kuma jiran wani za mu yi ba. Mune da kanmu, kuma al’marin yana hannunmu ne!


𝐇𝐚𝐦𝐢𝐝𝐢𝐲𝐲𝐮𝐧 𝐏𝐫𝐞𝐬𝐬

𝟏𝟗/𝐉𝐚𝐧/𝟐𝟎𝟐𝟑

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post