[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Wannan magana da Farfesa Ibrahim Maƙari ya faɗa ainihin sa hadisin Annabi ﷺ ne, inda ya ce...
إن من أشراط الساعة أن يلتمس العلم عند الأصاغر
" Lallai yana daga alamun tashin ƙiyama ya zama ana neman ilimi a wajen ( الاصاغر) wannan kalma a yaren larabci yana nufin yara ma su ƙananan shekaru, amma kuma fassara shi a haka ya saɓa wa fassaran da Malamai magabata waɗanda duniya ta ba da shaida a kan Malantan su suka yi.
An tambayi Abdullahi bn Mubarak a kan me Annabi ﷺ yake nufi da الاصاغر a cikin wannan hadisi? Sai ya ce..
الَّذِينَ يَقُولُونَ بِرَأْيِهِمْ، فَأَمَّا صَغِيرٌ يَرْوِي عَنْ كَبِيرٍ; فَلَيْسَ بِصَغِيرٍ ".
" Sune waɗanda suke faɗin abu da ra'ayin su, amma yaro ƙarami idan ya ruwaito magana daga babba ba za a ƙira shi yaro "
Ibrahim Al Harbi Rahimahullah ( ya rasu hijira na da shekaru 285 ) ya ce...
الصغير إذا أخذ بقول رسول الله والصحابة والتابعين فهو كبير، والشيخ الكبير إن ترك السنن فهو صغير"
" Yaro idan ya ɗauka daga maganan Annabi ﷺ da Sahabbai da Tabi'ai to shi ɗin babba ne, Tsoho mai yawan shekaru idan ya bar abubuwa da suka tabbata daga Annabi ﷺ to shi ɗin ya zama ƙarami "
Abu Umar ibn Abdul Barriy Allah ya masa Rahama ( ya rasu hijira na da shekaru 463 ) yace...
إن الصغير المذكور في الحديث إنما يراد به الذي يستفتى ولا علم عنده، وإن الكبير هو العالم في أي شيء كان، وقالوا: الجاهل صغير وإن كان شيخاً، والعالم كبير وإن كان حدثاً .."
" Yaro da aka ambata a cikin hadisin kawai wanda ake nufi shine wanda yake fatawa alhali bai da ilmi, babba shine wanda yake da ilmi ko da a menene, suka ce Jahili ƙanƙanin mutum ne ko da yana da yawan shekaru, masani shi babba ne a idon kowa ko da yana da ƙananan shekaru "
Sayyidina Umar ( RA) ya ce...
فإن العلم ليس على حداثة السن وقدمه؛ ولكن الله يضعه حيث يشا
" Shifa ilimi ba a ƙanƙantan shekaru ne ko yawan sa ba, shi Allah yana sanya shi yadda ya so "
A ƙarshe ina addu'a wa Farfesa cewa duk abin da yake kai wanda ba daidai ba Allah ya ganar da shi ya azurta shi da gyarawa ya yafe masa.
Allah Ameen 🤲
Ahmad Muhammad Makama