[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Akwai hadisai masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah(S)
Kan Falalar Son Sayyida Fatima (a,s) Ga wasu
Daga cikin hadisan:
1-Manzon Allah ya ce,
“Duk wanda yaso Fatima ‘ya ta to zai kasance cikin
Aljanna tare da ni.”
A wani hadisi kuma Manzon Allah(S)
ya ce, “Son Fatima yana Amfanar mutum a
wajaje Dari daga cikin wajajen Akwai lokacin
mutuwarsa, zamansa A kabari, Ranar kiyama,kan siradi da kuma wajen Hisabi.
A wata Ruwaye ya zo
Akan cewa son Fatima Alama ce ta Imani, kinta
kuma Alama ce ta munafirci.
A wata ruwaya
kuma Manzon Allah(S) ya ce, “An sanya ma Fatima
suna Fatima domin Allah ta’ala ya Bata Damar Fansar Masoyanta Daga Wuta Zuwa Aljannah.
Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareta, tare da mahaifinta, da
mahaifiyarta da mijinta, da ƴaƴanta.
Allah yabiya da alkhairai
ReplyDelete