[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Jiya Asabar 14 ga watan Januwari wasu daga cikin almajiran jagoran harkar musulunci a Nijeriya shaikh Ibrahim Zakzaky (H) karkashin jagorancin Dr. Sunusi Abdulkadir Koki suka kai wata ziyarar sadar da zumunci ga kungiyar Ansarudden (ta yan Tijjaniya zalla) a ofishinta dake babbar birnin tarayya Abuja. Makasudin ziyarar shine kusantar juna domin samar da kyakkyawar alaka da kuma hadin kai tsakanin al'ummar musulmi baki daya.
Babban wakilin kungiyar na kasa ketare baki daya Shaikh Alqasim Yahaya Yawuri (Wanda kuma yake aure ga daya daga cikin tsatson shehu Ibrahim Inyass RTA) shine ya tarbi tawagar yan'uwa din a ofishinsu dake unguwar A.Y.A a cikin birnin Abuja.
Dr. Sunusi Abdukadir Koki da yan'uwa dake tare dashi sun samu kyakkyawar tarba tare da samun isasshen lokaci wajen yin jawabi masu muhimmanci da gamsarwa.
Game da maqasudin ziyarar tasu kuwa Dr. Sunusi ya bayyana cewar maqasudin shine domin karfafa alaka ta zumunci da kuma samun kusantar juna, wanda zai sa kowa ya fahimci abin da dan'uwansa musulmi yake yi.
Sannan kuma Dr. Sunusi ya isar masa da sakon da'awar da shaikh Zakzaky (H) yake yi da kuma waki'ar Buhar ta 2015 da kuma muhimmancin hadin kai tsakanin musulmi baki daya.
A nasa bangaren Alhaji Yahaya Alkasim yayi jawabai masu matukar muhimmancin gaske ga tawagar yan'uwan da kuma musulmi baki daya. Ya fara da yin godiya game da wannan ziyarar ta yan'uwa almajiran shaikh Zakzaky garesu.
Shi ma ya bayyana cewar lallai akwai matukar bukatar samun hadin kai tsakanin musulmi baki daya. Ya kara da cewar musulunci dai abu daya ne kuma gida daya ne, idan ma akwai sabani a wasu wuraren to lallai abin da ya hadamu ya fi sabanin namu yawa.
Alhaji Yahaya Alkasim Yawuri ya bai wa Dr. Sunusi sakon gaisuwa da jinjinarsa tare kuma da yin jajensa ga jagorar Harkar musulunci a Nijeriya Shaikh Ibrahim Zakzaky (H).
Ya bayyana matukar damuwa da alhinisa da rashin jin dadinsa game da waki'ar da ta faru a Zaria a 2015 yayi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka yi shahada a waki'ar.
Ita dai kungiyar Ansaruddeen Tijjaniyya maulana shehu Ibrahim Inyass (rta) da kansa ne ya assasata, kuma cibiyar kungiyar na nan a birnin Kaulaha dake kasar Senegal.
A karshe ya bayyana cewar wannan alakar tabbas ta kullu kenan har abada, kuma za'a cigaba da tuntubar juna lokaci bayan lokaci, sannan suka yi musanyar lambobin waya a tsakanunsu domin cigaba da mu'amala.
--------
Nasir Abu Muhammad