DR. Sunusi ya kai wa Professor Sadiq Abba na Jami'ar Abuja ziyara har gida....!!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]



Ranar lahadi 16/01/2023 da misalin karfe daya da rabi na rana ne Dr. Sunusi Abdulkadir Koki  da wasu yanuwa suka kai wa babban malamin Jami'ar nan dake koyarwa a Jami'ar Abuja, waton Farfesa Sadiq Abba ziyara har gidansa.

Cikin nishadi da farin ciki farfesa Sadiq Abba ya tarbi Dr. Sunusi Abdulkadir da tawagarsa a gidansa dake unguwar Gwagwalada cikin birnin Abuja.

Dr. Sunusi yq bayyana wa farfesan cewar ziyarar tasu ta sadar da zumunci ce da kuma karfafar juna game da hadin kan musulmi baki daya. Ya bayyana cewar kusantar juna tabbas na kawo fahimtar juna. Sannan ya jinjina wa Farfesan bisa kokarinsa na yin aiki tukuru domin ganin an samu hadin kan musulmi .


Dr. Sunusi ya jajanta wa farfesan tare da kungiyar ASU bisa kwashe watanni suna yajin aikin neman hakkinsu amma kuma gwamnati tayi biris dasu, duk da kuma irin gagarumar gudunmuwar da suke bayarwa a kasar nan.

Dr. Sunusi ya bayyana wa farfesan cewar lallai su dage domin suna da rawar da zasu taka sosai wajen kawo sauyi da cigaba a kasar nan baki daya.

A karshe Dr. Sunusi ya isar masa da gaisuwar jagoran harkar musulunci a Nijeriya shaikh Ibrahim Zakzaky (H) da kuma yan'uwa baki daya.


A nasa bangaren, Professor Sadiq Abba ya nuna matukar godiyarsa da jin dadinsa game da wannan ziyarar da almajiran shaikh Zakzaky (H) suka kawo masa karkashin jagorancin Dr. Sunusi. 


Farfesa Sadiq Abba ya fara ne da tambayar labarin shaikh Zakzaky da lafiyarsa? 

Farfesa ya bayyana cewar ai hadin kai tsakanin musulmi wajibi ne kuma aiki ne da ya hau kan duk musulmi, don haka ayyukansa da yake yi yana sauke wajibinsa ne.

A karshe Dr.Sunusi da Farfesa Sadiq Abba sun tattauna kan lamura da batutuwan ilimi masu yawa, sannan suka yi musanyen sadarwa aka dauki hotuna. Sannan farfesa yace wa Dr. Sunusi da lallai ya isar masa da gaisuwarsa zuwa ga Sheikh Zakzaky (H).

----------‐-

Nasir Abu Muhammad

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post