Dr. Sunusi Abdulkadir Koki ya ziyarcibabban shehin Tijjaniya a garin Lokoja !!!




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


 Nasir Isa Ali



Ranar Laraba a wannan makon 25/01/2023 wanda ya yi dai dai da 3 ga watan Rajab /1444 (HJ)  da misalin karfe 12 na rana shaikh Dr. Sunusi Abdulkadir Koki ya ziyarci babban shehin Darikar Tijjaniya dake birnin Lokaja a jihar Kogi, waton shaikh Shu’aibu Kanchi Lokoja a zawiyarsa domin sada zumunci da kuma isar masa da sakon da'awar jagoran harkar musulunci a Nijeriya shaikh Ibrahim Zakzaky (H)


Shaikh Dr. Sunusi Abdulkadir Koki da tawgarsa sun samu kyakkyawar tarba daga shehin da muridansa. 

Dr. Sunusi ya fara da gabatar da kansa ga shehi, sannan kuma ya Bayyana masa maqasudin ziyarar tasa, waton sadar da zumunci domin kulla alaka da kuma kusantar juna domin kawo fahimta da hadin kai tsakanin musulmi baki daya. 

Ziyartar juna na saurin kusanto da musulmi kusa da juna, kuma hakan na kara sawa kowa ya fahimci abin da yanuwansa musulmi suke yi wannan kuma zai kawo fahimtar juna da kuma girmama juna.


Dr. Sunusi ya kara da cewar "mu almajiran mallam Zakzaky (H) muna kai wa malamai da shehunnai ziyara ne domin neman tabarrukin shehunnai da kuma isar musu da sakon da'awar da jagoranmu yake yi, wannan ziyarar da mu almajiran mallam Zakzaky muke kai wa maluman musulunci da shehunnai a gidaje da zawiyoyinsu yana daga cikin abin da jagoran namu ya koya mana na girmama maluma da kuma neman albarka da tabarrukinsu.


Dr. ya Kara da cewa wannan bala’i da masifu da kala kalae da ke fama dasu a cikin kasar nan, lallai malamai suna da rawar da zasu taka sosai wajen tarbiyartar da almajirai da muridansu domin su koma ga Allah ta'ala kamar dai yadda jagoranmu shaikh Zakzaky ya kwashe shekaru sama da 40 yana kirar alumma da ta koma ga tsarin Allah da manzonsa, kuma wannan ita ce hanya daya tilo wacce zata kai musulmi da sauran alumma zuwa ga tsira in ji Dr. Sunusi Abdulkadir Koki. 

Sannan Dr. Sunusi ya gabatar wa shehin gaisuwa ta musamman daga jagoran harkar musulunci a Nijeriya shaikh Ibrahim Zakzaky (H)


A nasa bangaren shaikh Shu'aibu ya bayyana matukar farincikinsa da godiyarsa bisa wannan ziyarar ta zumunci da girmamawa wacce almajiran shehin Zakzaky suka kawo masa.

Ya yi jinjina matuka ga ayyukan da shaikh Zakzaky yake gabatarwa, sannan yace a mika masa gaisuwarsa da jinjinarsa zuwa ga shaikh Zakzaky (H) 

Sannan a karshe aka dauki hotuna tare da yiwa tawagar yan'uwa rakiya.

-----

Nasir Abu Muhammad

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post