@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@
𝐒𝐡𝐞𝐢𝐤𝐡 𝐙𝐚𝐤𝐳𝐚𝐤𝐲 (𝐇)
To, kun ga in Allah Ta’ala ya gwada ka, abin da yake so da kai ka ci jarabawa, in ka ci shi kenan an gama, sai lambar yabo. To, dole kuwa in za a jarabta ka dole kuwa a jarabtaka da abin da yake da wahala.
Kun san ko jarabawar da ake yi a makarantu, ya jarabawa take? In aka rubuta jarabawa kowa ya ci dari bisa dari ya zama jarabawa?
Lokacin ina makaranta a Kano, ni dai bai koyar da ni ba, amma mutumin yana da dan tavin hankali ana ce masa Abdulqadir, wani Bamisire.
Wai shi jarabawarsa, imma Mi'a bil Mi'a wa imma Sifir. Haka yake maki. In ya qyallara idonsa, da ma ba ya gani sosai, in ya ga rubutunka na da kyau sai ya ce Mi'a Fauqal Mi'a.
Kuma ko ka amsa daidai in ya ga rubutun gaja-gaja sai ya ce sifir.
Shi makinsa kenan, ko dai ka ci dari bisa dari ko ka ci sifili! Ni bai koyar da ajinmu ba, amma dai a shekarar
da muke ya koyar da wasu, tunda muna da azuzuwa hudu ne a shekara guda ABCD, to ya koyar da 'yan C da B suna ta kuka.
Wani ya iya amma kuma dai ya yi rashin sa'a ran nan ziro ya samu, wani kuma ya yi sa'a ya sami dari, wani ma bai iya komai ba ya ce shi gaskiya bai gane Arabiyya dn nan ba. Sai ya je ya sami wani littafi ya haddace wani shafi, sai ya zo ya rubata shafin. Sai ya ce duk Mi'a.
wannan ba jarabawa bace. Kyawun jarabawa (shi ne) ya zamana an tambaye ka wani abu ne wanda yake ko za ka iya ci ko za ka iya faduwa.
In ya zama duk ci za ka yi, to ba jarabawa bace. In ya zama kuma duk faduwa za ka yi, shi ma ba jarabawa bace. “La yu kallifullahu nafsan illa wus'aha”.
Saboda haka duk lokacin da aka sa jarabawa jarabawa da za ka iya ci.
Kuma zai yiwu ma ka ci duk. To za a jarabtaka ne da abubuwa da daman gaske, “Wala Nabluwannakum bi Shai'in Minal Khaufi wal Ju'i wa Naqsin Minal Amwali wal Amfusi Wasthamarat wa BasshirisSaabireen”.
To ka ga jarabawowin kenan. Tsoro, za a jarabtaka da tsoro. Kun ga na farko akwai waxanda aka firgitar da su. Aka ce masu “Innannaasa qad Jama'ulakum Fakhshauhum”. Sai suka ji tsaro? “Fazadahum Imanan wa Qalu Hasbunallahu wa Ni’imal Wakeel”.
Su muminai ne aka zo ana ba su tsoro. Wani ya ce, "a'a kai! Za ku cimma runduna, ta shirya sosai, mayaqa majiya qarfi da muggan makamai."
Wai yana so ya ba su tsoro. Kai yadda na gan ku nan za su yi loma daya ne da ku. Shi ya dauka muminai za su ji tsoro ne.
Kawai sai ya ga ana ta fara'a. Ana Malam ya? Ashe yau kuma Alhamdulillahi za mu yi shahada, masha Allahu! Wannan shi ne abin da Allah da Manzo suka yi mana alqawari. Kuma Allah da Manzo sun yi gaskiya.
Koda yake da Hausa ne. Ana cewa a cikin Alqur'ani ba a fadin haka nan.
Idan ka ce Allah da Manzonsa sai ka ce ya yi gaskiya. “Wallahu wa Rasuluhu Ahaqqu Anyurduhu”. Manzo ya ji wani ya ce Allah da Manzonsa, sai ya ce huma. Sai ya ce ka munana magana, ba a gwama Allah da kowa.
“Hazaa ma Wa'adanallahu Warasuluhu wa Sadaqallahu Warasuluhu”. Ba a cewa “Wasadaqaa” ba. “Wallahu wa Rasuluhu Ahaqqu Anyurduhu”, ba ‘Yurdouhuma’ ba. Wato in ka fasdi Allah, ba ka gwama shi da kowa.
𝐇𝐚𝐦𝐢𝐝𝐢𝐲𝐲𝐮𝐧 𝐏𝐫𝐞𝐬𝐬