[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Kowa zai so sanin yaya aka yi Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) ya fara wannan Da’awa tasa, wato meye dalili, ko ya aka yi tunanin fara yin Da’awar ya zo masa?
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha amsa wannan tambaya ga ‘yan jaridu, yakan ce, shi a farko bai taba tunanin zai zama mai Da’awa ko ya zama malamin addini ba, tunaninsa shi ne in ya gama karatunsa na boko zai zama ma’aikacin gwamnati ne ko malamin jami’a, domin rayuwar ma’aikatan gwamnati da ta malaman jami’a tana burge shi, rayuwa ce ta natsuwa wacce ba hayaniya a cikinta, kuma shi yana sha’awar rayuwa ta kadaici da natsuwa, ba ya son a san shi ko ya zama wani fitaccen mutum, domin ba ya son hayaniya da dawainiyoyi da yawa.
To, ya aka yi tunanin Shaikh Zakzaky (H) ya canza daga zama ma’aikacin gwamnati ya koma malamin addini mai Da’awa da gwagwarmaya? Shaikh Zakzaky ya amsa tambayar kamar haka; “Ina iya cewa (zama mai Da’awa da na yi) qaddara ce ta Ubangiji da kuma ayyukan wadanda suke ganin za su ga bayana, su lalata ni, su hana ni magana….. Domin lokacin da na shiga jami’a, akwai qalubale da yawa da suke fuskantar Musulunci, akwai masu aqidar gurguzu a wancan lokacin, (yanzu babu su ya’alla a harabobin jami’a ne ko a ko’ina), a wancan lokacin suna caccakar duk wani abu da ya shafi Musulunci da shi kansa addini gaba daya.
“To, sakamakon na taso da ilimin addinin musulunci, na san suna sukar Musulunci ne kan abin da bai da laifi, suna da aqidar cewa addini kamar qwaya ce mai bugarwa ga mutane, kuma da shi ake fakewa ana zaluntar jama’a, suna kawo misali da sarakunan da suke da mata barkatai da sakakoki, kamar wannan kawai Musulunci ya qunsa, sai muka ga bai kamata mu yi shiru kan irin wannan zarge-zarge ba, dan haka muka fara kare addini, ta haka wannan Da’awa ta fara, wato kare addini, kuma a lokaci guda da koyar da mutane haqiqanin manufofin addinin.
“(Domin) mun gano akwai ‘ya’yan musulmi da ba su san mene ne addinin Musulunci ba, wanda masu wannan farfaganda za su iya yaudararsu da wadannan aqidu, hasali ma da dama ko mafi rinjayen (masu aqidar Gurguzun) ‘ya’yan musulmi ne suka dawo suna zargin Musulunci da zaluntar dan adam, alhali a daukacin tarihin dan adam ba wata aqida ko tunanin da ya tseratar da dan adam kamar Musulunci.
“Wani bangare da suka fi kwarmato akai shi ne batun mata, sun zargi Musulunci da tauye mata, amma bisa dan ilimin da muke da shi, mun san wannan ba gaskiya bane, duk da cewa abin da wadansu musulmi suke yi ga mata za a ga kamar haka (musulunci yake), amma wannan ba yana nufin Musulunci ne ya koyar da hakan ba. To, zan iya cewa da haka muka fara (wannan Da’awa) a jami’a, kuma ga alama (abin da muke yin ba ya yi musu dadi), ba su son wannan ci gaba da aka samu, don haka suka fara musguna mana tun muna dalibta, ta kai ga an kama mu an tsare…
“Kuma ina iya cewa wannan (Da’awa din) qaddara ce daga Allah, idan muka karanta tarihin Annabi Musa (AS), za mu ga yana qoqarin kare dan qabilarsa ne (ta kai ga) ya banke ma’aikacin tsaro na Fir’auna ya mutu. Wannan ya tilastawa Annabi Musa (AS) yin hijira, kuma akan hanyarsa ta dawowa ne Allah ya yi masa wahayi da Annabta, wannan qaddara ce ta Ubangiji cewa hakan zai faru. A nawa gefen ma ina iya cewa qaddara ce ta Ubangiji cewa hakan za ta faru, amma ban taba tunanin faruwar hakan ba, ban taba tunanin zan zama malamin addinin Musulunci ba, abin da kawai na yi tsammani shi ne ko dai in zama ma’aikacin gwamnati, ko malamin jami’a, sai na tsinci kaina a abin da nake kai a yanzu”.
Bayan Shaikh Zakzaky (H) ya soma gwagwarmaya da masu aqidar Gurguzu da ke sukar fikirar addini, tare da tuhumar musulunci da kushe shi kan abubuwa da dama, wanda kuma cikin qanqanin lokaci suna ta gurbata aqidun ‘ya’yan musulmi ta hanyar falsafa da hikimomi irin nasu, sai ya zamo in Shaikh Zakzaky (H) ya dauki Alqur’ani yana karantawa sai ya ji kamar da shi ake magana, kamar Allah Ta’ala yana umartarsa ne da ya tashi ya kare addini ta hanyar karantar da mutane haqiqanin addini da nuna musu hanyar shiriya.
A wata hira da “Mujallar Gwagwarmaya” Shaikh Zakzaky (H) yana cewa; “A lokacin in na karanci Alqur’ani sai in riqa fahimtarsa ta wata mahanga da ada can ni ban gane ba. Ba zan manta ba, a lokacin har nakan riqa kallon aya sai ina ganin kamar a lokacin aka sauqar da ita… wato sai Allah ya sanya mini fahimta, in na karanta (aya) sai in ga kamar ana magana da ni ne!”
Kenan, idan mun lura da wadannan bayanai, za mu ga cewa abubuwa biyu ne suka zamo asasin wannan Da’awa ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), qoqarin kare addinin Musulunci da fikirarsa don ceto al’ummar musulmi daga gurbacewar aqida, da kuma qaddarawar Allah Ta’ala wacce ya riga ya zartar, wannan su ne tushe ko mu ce asalin abin da ya sa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara wannan kira na Harka Islamiyyah a Nijeriya.
To, mene ne hadafin Harka Islamiyya din?
Amsa na nan a cikin littafin SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH.