Gangami hade da Muzaharar #RealeseZakzakyPassport! ke gudana yanzu Haka a Abuja.
Matasa masu fafutukar neman 'yancin Jagora Sayyid Zakzaky (H), sun sake fitowa kamar yadda suka Saba, suna sake kira, ga gwamnatin Buhari dasu gaggauta sakin Fasfo din Jagora Sayyid Zakzaky (H) damai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim, su tafi neman lafiya,
An soma wannan gangami ne daga bakin Masallacin Wuse Market sannan aka wuce da Muzahara Cikin tsari da nutsuwa,
Inda Masu Muzaharar suke tafiya, suna rera wakokin, Basu yadda dacigaba da rike Fasfo din Sheikh Zakzaky (H) ba, tare dana Mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim,
27, January 2023.
Tags:
Labaran Duniya