Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, SSS sun mamaye hedikwatar babban bankin Najeriya, CBN inda suka kwace ofishin gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa a kwai wata jiƙaƙƙiya tsakanin jami’an na SSS deer da Emefiele kan zargin tallafawa ta’addanci.
A baya dai hukumar ta DSS ta nemi kotu ta bata izinin kama Emefiele amma ya fice daga kasar domin hutun shekara da zai kare a gobe 17 ga watan Janairu.
Sai dai a watan Disamba ne babbar kotun birnin tarayya ta haramtawa DSS kama, gayyata, ko kuma tsare Emefiele.
Amma kuma a yau Litinin da jami’an DSS da suka isa hedikwatar ta CBN, sun shigo da motoci kusan 20 dauke da jami’an tsaro.
Jami’an sun kuma hana duk ma’aikatan bankin shiga ofishin Emefiele.
Peter Afunanya, mai magana da yawun SSS, har bai amsa sakon neman bahasi da wakilin Daily Nigeria ya aike masa ba.