Da gaske ne maganar cewa Shaikh Zakzaky ba dan siyasa bane, kuma ba zai taba zama dan siyasa ba in har siyasa da ma'anar siyasar Nijeriya da ake yi ???

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Kila idan na ce Ki ji tsoron Allah, za ki ga kamar babu bukatar hakan. Kamar yadda in aka ce ku ji tsoron Allah ku kan ce a ce ma wani ba ku ba.


Amma gaskiya magana da dukkan girmamawa karya kike yi.


Da gaske ne maganar cewa Shaikh Zakzaky ba dan siyasa bane, kuma ba zai taba zama dan siyasa ba in har siyasa da ma'anar siyasar Nijeriya da ake yi ne, babu wannan ranar InshaAllahul Azeem.


Amma siyasar rayuwa da zamantakewa, irin wanda Amirulmuminin (AS) da sauran Tsarkaka (AS) suka koyar, Shaikh Zakzaky ya iya wannan, kuma yana kamantawa. A kan wanna ne ma yan siyasa da yan fim da yan Darika da sarakuna da malamai da almajirai suke ziyartarsa yake basu kulawa.


Na rantse miki da Allah Ta'ala, duk wadanda suke zuwa su ziyarci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) din nan su suke nemar a basu damar hakan, kuma wadanda ake ba damar ba su fi kashi 1 cikin 10 na masu neman zuwa din ba! Don haka ba ke kawai ba, har masu irin ra'ayinki, yana da kyau su fahimci lallai ba Shaikh Zakzaky ne ke gayyatar yan siyasa ko wasunsu ba, nema suke yi da kansu ake basu. Akwai ma wadanda suke zuwa din su nemi kar a saka hotonsu kuma a yi hakan. Wasu ma ko hoton ba a dauka bare a yada.


Da ace shi ke bukatarsu zai je wajensu ne kamar yadda wasu Malaman ke tashi su je su roki a basu damar ganawa da yan siyasa, har da mai zuwa wajen su Osinbajo ma, su gana da su. Wasu a basu kudi ma su karɓa, sabanin Shaikh Zakzaky da wani bai isa yace ya taba bashi kudi ko ta wace hanya a Yan siyasar kasar nan ya karɓa ba.


Sannan batun girmamawa, shima hasashenki ne. Kuma don Allah me ya kai dadin jan mabiyansa Sallah idan suka ziyarce shi? Shin rakiya zai fi ma mabiyi daɗi a kan a ja shi Sallah da addu'a?


Tunda kina Ikirarin bin addini sahihi, ya kamata kiyaye hukunci da zato ko jita-jita, domin za a muku Hisabi a kan hakan. Me yasa duk wanda ya taba zuwa wajen Shaikh Zakzaky (H) a cikin almajiransa babban burinsa shine Allah Ya maimaita masa? Ba a girmama shi zai samu hakan?


Ni nan da ba kowan kowa ba, face yaro ƙarami, almajiri dan almajirin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), bayan fitowar Shaikh Zakzaky (H) na samu ziyarartarsa kusan sau 5, kuma na sha fada cewa ban taba ganin mai mutunta mutane da saukar da kai garesu kamar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba. Yadda Shaikh Zakzaky ke tsayawa da almajiransa a yi hira da raha, a tattauna, ya basu shawarwari har a kan rayuwarsu da uwa uba addininsu, wallahi ko mahaifanmu sai haka.


Yadda yake damuwa da mutane da damuwarsu ba zai misaltu ba. Don haka ban san wane almajirinsa ne za ki ce masa ya fi ba waninsa kulawa ya yarda miki ba. Illa kowa da irin kulawar da ke bayyana an bashi. Bana tsammanin rakiyar baki kulawa ce da almajirin Shaikh Zakzaky zai bukaci ya masa, duk da cewa yana yi din ma a wasu lokuttan. Kamar yadda ba bukatar sai Shaikh Zakzaky ya zo yana nunawa Burazu hoton Husainiyya da aka rushe ko gidansa, alhali ba abin da basu sani ba kan wannan.


Na dauka mutuwar Ustaz Hamza zai sa akalla ku fahimci cewa bata lokaci ne shagaltar da kai wajen kokarin kushe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da da'awarsa, domin irin hakan ba abin da ke karawa Da'awar sai fahimta a zukatanmu bayin Allah masu rabo.


Allah Ya datar da mu alfarmar Annabi da Ahlulbaiti (AS).


— Saifullahi M Kabir

24/1/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post