CBN: Aikin Hankali ko Aikin Rashin Tunani !!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


(Maimaici) Nayi Wannan Rubutun A Ranar 27 Ga Watan Oktoba 2022.✍️.


AIKIN HANKALI: A Shekarar 2014 Zamanin Jonathan Gudluck a Lokacin Da Najeriya Ta Cika Shekaru 100 Na Hade Kasar Tsakanin Kudu Da Arewa (Amalgamation) Gwamnati Ta Canja Fasalin Naira 100, Inda Ta fito da sabbi, Babban Bankin Najeriya Yace Za'a ci gaba da kashe Sabon Kudin Da Tsohon Kudin A Lokaci Guda Har Tsoffin Su Bace.


AIKIN HANKALI: Hakama A kayi a Shekarar 2010 Duka Dai a Zamanin Gudluck, A Lokacin Bikin Cikar Najeriya Shekaru 50 Da Samun Yanci Kan Najeriya, Babban Bankin Najeriya (CBN) Yayi Sauye-sauye A Takardar Kudi Ta Naira Hamsim, Hakanan (CBN) Yace Za'a Ci Gaba Da Kashe Tsohuwar Takardar Kudin Da Sabuwar Har Tsohuwar Takardar Naira 50 Din Ta Bace, Ma'ana Idan Ta Shiga Banki Bazata Sake Fitowa  Ba.


AIKIN RASHI TUNANI: A Yanzu CBN ya ba da wa’adin kwana 47 a mai da tsoffin kudin da za a sauya banki. Wannan Canji Koda Yana Da Kyau Wadannan Kwanaki Sunyi Mutukar Kadan.


Haka Ya Faru A Lokacin Mulkin Soja Na Janar Muhammadu Buhari A Watan Fabrairu 1984, Babban Bankin Najeriya Ya Bayar Da Umarnin Sauya Kudin Na Naira A Sati Biyu Rak, Sannan Najeriya Nada Yawan Jama'a ( 81.45 million) Kawai A Yanzu Kuwa Najeriya Nada Yawan mutane (217,947,709).


A Lokacin Kudin Takardun Naira Ya Soma Daga Sulai Biyar ta Takarda Zuwa Naira 20, A Zamanin Mutane Sun Mutukar Shan Bakar Walaha Wasu kuwa Karyewar Arzikin su Kenan Har Abada.


Kamata Yayi Babban Bankin Najeriya (CBN) Ya Kara dogon Lokaci Tare Da Umarnin Karbar Sabon Kudin da Tsohon A Lokaci Guda, Kamar Yadda Yayi 2010/2014 Domin Kauce Wahallahalu Da Jama'a Ka Iya Fuskanta. 


Hakika Duk Wanda Yasan Abinda Ya Faru A Watan Fabrairun 1984 Ko Yake Da Tarihin Abinda Ya Afku, Bazai Samu Natsuwa Da Wannan Canjin Kudin da Bayar da Wannan Takaitaccen Wa'adin Ba.


Saliadeen Sicey ✍️

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post