Canjin Kudi Ya Fara Jefa Fargaba A Zukatan Al'ummar Nijeriya....!!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Daga Saifullahi M Kabir.


Kwanaki 10 ya rage wa'adin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bada ya cika, na rashin karɓar tsofaffin takardun kuɗaɗen da suka haɗa da Naira 200, N500 da N1,000. Sai dai tun yanzu, mutane na ta zullumi kan yadda rayuwa za ta kasance na tsawon lokacin da za a gama hada-hadar daina amsar kuɗaɗen, a samu sababbin su game cikin al'umma.


Da safiyar Asabar din nan wani mai sana'ar tura kudi ta POS a garin Saminaka ta jihar Kaduna, yake shaida min cewa, daga jibi Litini da safe zai tattara duk kuɗaɗen da ke wajensa ya kai su Banki ya shigar, sannan kuma ya rufe shagonsa har sai abin da hali ya bada.


Ya ce, saboda Bankin Keystone wanda ya fi hulda da su, sun shaida masa cewa ranar Laraba 25 ga watan Junairun 2023 din nan mai zuwa, ita ce ranar da za su daina amsar kudade barkatai, su ma za su yi kokarin tattara duk tsofaffin kudadensu su kai su Babban Bankin Ƙasa tun kafin ranar 31/1/2023 da Bankin ya ƙayyade wa'adi.


Masu shaguna da dama sun bayyana cewa daga ranar Litinin mai zuwa za su rufe shagunansu ne, domin ko sun fito da nufin sayar da kaya ba zai yiwu su karɓi tsofaffin takardun kuɗaɗen ba, kuma mutane da yawa babu sababbin kuɗaɗen a hannunsu.


Ko da yake Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya yi kasheji ga sauran Bankuna a kan su riƙa sanya sababbin kuɗaɗe a Mashinan cire kudinsu (ATM), sannan kuma ya ja hankali ga mutane kan su dena amsar tsofaffin kuɗaɗe daga Bankunan, amma har yanzu su kansu Bankunan suna korafin cewa ba a basu sababbin kuɗaɗen da za su isa su aiwatar da wannan ƙudirin ba.


Har yau ɗin nan, mafi yawan Bankuna idan ka je cire kuɗi tsofaffin takardu ake samu. Don haka har zuwa yau da ya rage kwanaki 10 a rufe amsarsu, mafi yawan al'ummar Nijeriya ba su mallaki ko takarda guda ɗaya na sabon kuɗin ba, a yayin da rabin 'yan Nijeriya ko kalar sabon takardun kuɗin ba su taba gani a zahiri ba sai a hotunan ƙaddamar da su da aka yi.


Mafi yawan 'yan Nijeriya ba su da Asusun Banki, musamman 'yan ƙauyuka da kuma masu kananan sana'o'i. A yayin da aka rasa takardun kuɗaɗe a hannu, ta wace hanya za a bi a sayi kayayyakin siyarwarsu ko su su sayi abin bukatarsu daga wajen wani?


Wannan ne dalilin da zai sa shaguna da dama su rufe, a koma gida a yi zaman jangwam har zuwa lokacin da abubuwa za su daidaita a fara fitowa, kafin nan da yawa sun cinye ɗan tanajin da suka yi na abinci. Wanda in an dawo daidai kuma akwai yiwuwar kara hauhawar farashin kayayyaki saboda tsaikon kasuwancin da za a samu a wannan tsawon lokaci.


To, wai ma zuwa yaushe ne wannan halin da za a shiga zai lafa?


Kila sai lokacin da kowane ɗan Nijeriya ya mallaki Asusun Banki, ta yadda komai zai saya komai kankantarsa zai tura ne ta bankin, inda a wannan lokacin kuma zai zama ko da 500 ya tura, Banki za ta caje shi haraji kala uku, wanda ba a ganinsu sai kana da Manhajin Banki (Application) ko idan ka ga an zare maka kudi ba gaira ba dalili a dunkule, wanda sune: FIP Charges, N53; da VAT wanda yana kai N6 zuwa N10; da ma wani da kwanan nan na fara ganinsa mai suna VERVE Maintainance Fee, wanda yake farawa daga N50 har zuwa N1000 ko fiye, gwargwadon girman 'transaction' dinka.


A wannan lokacin, akalla idan ka sayi abu na N1000, Banki za ta cire harajin kusan Naira 100 a ciki, wanda za su yi raba daidai tsakanin Bankin da Hukumar Nijeriya.


Idan ba haka ba, sai sadda aka buga takardun kuɗaɗe suka wadaci al'ummar Nijeriya, wanda shi kuma wannan da wuya sosai ya auku nan da kankanin lokaci.


Kila kuma sai ranar da wata gwamnatin ta zo, in bata dora a kan salon gwamnatin Shugaba Buhari ba, ta samar da wani sassaukan yanayi da zai ragewa 'yan Nijeriya radadin da wannan canjin kuɗin na Buhari ya jefa su a ciki.


Shawara ta ga mutane:


A fa fitar da kudade a kai Banki a ajiye, a kuma kiyayi cigaba da karban tsofaffi kafin kurewar lokaci. A tanaji abinci gwargwadon hali a gida, da sauran kayan bukatu. A kuma bi da addu'a, wanda ya cutar da mu bisa nufin ƙeta da mugunta, Allah Ya mana maganinsa duniya da lahira. Allah Ya saukaka mana wannan hali da azzalumai suka jefa mu a ciki da gangan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post