CANJIN KUDI... Malam Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky Hafizahullah, Yayi Shekara Sama da 40 yana Kiran wannan al-ummar zuwa komawa ga addinin Allah (T) ayi aiki da shari'ar allah ta'ala. akyale duk wani tsari wanda ya saba da na Allah.




Alhamdulillah, Ansamu masu amsa masa wannan kira Amma abin mamakin da ban takaicin shine akalla wadannan mijoriti din da basu amsa masa ba, koda basu taba ji daga gareshi ta hanyar jin muryar sa ba, Dole matukar mutum dan nijeriya ne zaiji daga almajiran sa, koda wucewa yazo yi watarana sai yaji ya kuma fahimci abinda ake cewa ko ta hanyar wake ne. 


Amma meyasa har kullum mutanen gari tamkar ana bude kwakwalen su a kwashe masu tunani, a zuba masu Wanda akeso aciki a mayar a rufe, lamarin akwai ban mamaki, yadda zaka kasa gane yadda akai hankalin da tunanin Yan nijeriya (Amawa) yake gushewa, ayi wasa da tunaninsu lafiya lau yadda ake so. Sun zo da wani rainin wayo wai shi boko haram, sungama wawaitar da al-umma Sunyi abinda sukeso, sai suka sake sabon salo wai kidinafin da fadan makiyaya, gefe duga Kuma zamfara da borno suna ta Kashe mutane, an kuma  kasa gane suwaye suke wannan aiki, wai wasune Yan bindiga dadi.


Daga cikin duk wadannan shirmen da rainin wayon, babu wanda malam Zakzaky bai fito ya bazar da Shirin nasu tun kafin suyi shi ba, duk lokacin da sukayi wani yunkuri na cutar da wannan al-ummar to Syed Zakzaky Yana baje shirinsu kafin ma suyi. Yanzu gashinan sun kara fito da wanin sabon shirin zaluntar bayin Allah, wai canjin kudi, wawaye kadai sune zasuyi tunanin cewa wannan canjin kudin ci gaba ne ga al-umma. Duk mai cikakken hankali da tunani yasan cewa anyi ne domin kara durkusa tattalin arziki da cutar da talakawa.


Ya Kai dan najeriya mafitarka daya ce, bayanta Kuma babu wata, ka kyale wannan macutan naka, da kake gani amatsayin maceta, ba zasu taba ceton ka ba. Addinin Allah shi kadai ne mafitar ka. kazo ka amsa kiran maulana Syed Zakzaky (H) .


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post