Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kama wasu mutum takwas da take zarginsu da alaƙa da 'yan fashin daji, tare da kwato makamai masu yawa.
A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandar jihar SP Mohammed Shehu ya fitar ya ce rundunar ta samu nasarar kwato bindigogi ƙirar gida 15 da harsasan bindigar AK-47 guda 146, da tabar wiwi, da kuma kuɗi da suka kai naira miliyan ɗaya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa rundunar 'yan sandan jihar ƙarƙashin jagorancin kwamishinan 'yan sanda na jihar CP Kolo Yosuf na ci gaba da samun nasara wajen daƙile munanan laifuka a faɗin jihar.Rundunar ta ce tun lokacin da ta ƙaddamar da yaƙi da ayyukan 'yan fashin daji a jihar ta samu nasarar kama fiye da mutum 200 da take zargi da alaƙa da ayyukan 'yan fashin daji, tare da ƙwoto makamai da harsasan bindigogi ƙirar AK-47 da na manyan bindigogin RPG, da na GPMG da na harba rokoki, da sauran bindigogi.Sanarwar ta ce wannan yunƙuri ya taimaka wajen daidaituwar zaman lafiyar jihar wadda a baya ta sha fama da matsalolin tsaro.
Haka kuma sanarwar ta zayyano wasu nasarori da ta ce ta samu a baya-bayan nan.
Ciki har da batun kama wasu makamai daga a cikin buhunhuna tsakanin Tsafe zuwa dajin Munhaye, tare da kama mutane da ake zargi da safarar makaman
barka da wannan lokaci daga APT Hausa
ReplyDelete