__Sheikh Ibrahim Al zakzaky (H)
"in da da wani abu da muke nufi ba wannan ba, bai gagare mu mu faɗa ba. Tsoron wa muke ji? Bindiga? Ta yi kaɗan! Ai an sha gwada mana ita. Har kwaraf-kwararaf a ja da nufin a harba an yi ya fi a ƙirga._
_"Kuma ba muna yi ne don mutane su bi mu ba. Wanda duk ya saurari wa'azinmu in ya ɗauka mai yi yana yi ne don a bi shi, don Allah don Annabi kar ya bi ni! .Cewa nake, a bi Allah, a bi Manzo. In yabi Allah ya bi Manzo toh Alhamdulillah dama Allah ya ɗora min na bi Allah da Manzo ya kuma ɗora mishi, ni kuma ina tunatarwa ne. Illa iyaka. Saboda haka ba buƙatar har in ɓoye wani abu wai don mutane su bi ni, kar ma a bi. In dai ka wa'aztu Alhamdulillah.
Ja'afar Muh'd
28-1-2023
Sheikh Zakzaky' Gallery