Yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane, da kuma matsin lamba mai tsananin gaske, ya yi matukar jefa fargaba a zukatan mazauna yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Kungiyoyin masu dauke da makamai suna fafutukar neman ballewar yankin, sai dai tantace alakar da ke tsakanin yunkurin masu fafutukar tabbatar da ‘yancin yankin da kuma ayyukan bata-gari lamari ne mai wahalar gaske.
tashetashen hankalin sun tilasta wa al’ummar kauyukan tserewa daga gidajensu domin neman mafakar da za su samu kwanciyar hankali har zuwa wasu ‘yan shekaru da suka gabata.
Kawuna ya gudu daga kauyen saboda wadannan mutane sun bukaci ya ba su kudade su sayi bindigogi da alburusai.
Kauyukanmu babu kowa saboda su ne ke iko da yankin a yanzu,” a cewar wani mutum da muke kiran sa Chike Anyikwa domin ba shi kariya daga ‘yan bindigar.
Yankin wanda ke kusa da dazuka, ‘yan bindigar sun kafa tasu gwamnatin a kauyen su Mista Anyikwa mai dadadden tarihi, da sauran kauyuka da dama a jihar Imo, da kuma jihar Anambra, wadda ke fama da yawan rikice-rikice.
An kara samun wasu sansanoni a wasu karin jahohi uku da suka hada da Abia, Ebonyi da jihar Enugu, wadanda suke yankin kudu maso gabashi inda mayakan ‘yan awaren ke fafutukar tabbatar kasar Biafra.
Masu dauke da makaman sun kwace iko daga hannun jami’an gwamnatoci da sarakunan gargajiyar yankin.
Idan wani na son yin aure ko gudanar da bikin binne mamaci, dole ne sai an nemi izinin su, kuma sai an biya kudi kafin a ba su izinin abin da suke son aiwatarwar.
Jagoran ‘yan tawayen shi ne ke da ikon warware duk wani sabani a tsakanin mazauna kauyukan da ma sauran batutuwa, kamar rikicin da ke shafar hakkin mallakar gonaki, wannan al’amari ne da ke bayyanuwa a fili cewa su ne ke da ikon yankunan.
Mista Anyikwa yana zaune ne a birnin Enugu, kuma kamar sauran dubban mutane, bai samu damar halartar bukukuwan Kirsimeti biyu da suka gabata a kauyensu ba, wanda hakan tamkar saba dokar dadaddiyar al’adar da aka gada kaka-da-kakanni ne na haduwa da ‘yan uwa da iyalai don gudanar da shagulgulan.
“Dangi suna gudanar da al’adar bikin aure a kauyenmu. Babu wanda ya halarta. Tsoro ba zai bar kowa ya halarta ba. Jami’an tsaro sun taho daga Owerri babban birnin jihar Imo, daga bisani kuma sun koma, kasancewar mafi yawan ofisoshin ‘yan sanda an lalata su.
A cewarsa, “Dokar da mutane suka sani ita ce wadda ‘yan bindigar da ba a tantance ko su wanene ba suka kafa, wadanda suke kiran kansu da ‘yan Biafra, amma mun san ba su ba ne”.
Yunkurin kirkiro kasar Biafra wani buri ne da ya jima a zukatan ‘yan kabilar Igbo da dama wadanda ke burin ganin yankin kudu maso gabashin Najeriya, da wasu daga cikin sassan jihar Delta, ya samu ‘yanci a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Kungiyar ‘yan awaren tabbatar da kasar Biafra (IPOB) na samun matukar goyon baya daga kasashen ketare.
Sakamakon yadda suka yi kaurin suna wajen kafa sana’oin dogaro da kai, ‘yan kabilar Igbo su ne kabila ta uku mafi yawa a Najeriya, wadanda suka kai kashi 15 cikin 100 na yawan al’ummar Najeriya mai yawan mutum kusan miliyan 217, kamar yadda kididdigar statista.com ta bayyana.
Kungiyar fafutukar ta fara gudanar da miyagun ayyukanta ne tun a shekarun 1960, a lokacin da wani jami’in soji dan kabilar Igbo, mai suna Emeka Odumegwu Ojukwu, ya ayyana kafa kasar Biafra biyo bayan kashe wasu ‘yan asalin yankin kudu maso gabashin kasar a arewacin Najeriya.
Sai dai yunkurin ballewar yankin ya ci tura bayan wani mummunan yakin basasa da aka shafe shekara uku ana gwabzawa, wanda ya yi sanadiyyar rayukan sama da mutane miliyan guda, da fama da matsananciyar yunwa da karancin kayayyakin kiwon lafiya.
Duk da rashin nasarar yunkurin na Laftana-Kanal Ojukwu ya fuskanta, amma burin ballewar ya ci gaba da wanzuwa a zukatan ‘yan awaren neman kafa kasar ta Biafra har zuwa wannan lokaci, inda a baya-bayan nan kungiyar ta yi wa kanta lakabin mai rajin tabbatar da ‘yancin alummar Biafra, wato IPOB a takaice cikin turancin Ingilishi.
Kungiyar wadda ‘yan asalin kabilar Igbo biyu mazauna kasar Birtaniya – Nnamdi Kanu da Uche Mefor suka kafa a shekarar 2012, a matsayin mai fafutukar lumana, daga baya sun kafa sashen mayaka na kungiyar, wadda aka fi sani da kungiyar tabbatar da tsaro ta Eastern Security Network ko kuma (ESN), a shekarar 2020.
Su na ikirarin tabbatar da kare ‘yan kabilar Igbo, koda yake masu sukar lamarin kungiyar sun bayyana cewa kungiyar ta kaddamar da wasu jerin hare-hare da suka yi sanadiyyar haifar da mummunar barna.
Gwamnatin Najeriya ta haramta ayyukan kungiyar IPOB, sannan kotu ta ayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta’addanci.
Masu sukar lamirin gwamnati sun ce amfani da karfin soji wajen kawar da kungiyar ya kara jefa fararen hula cikin halin tasku, wadanda sojoji suka mamaye kauyukansu, kuma aka tsare matasa har ma aka rinka kashe wasunsu bisa zargin su da goyon bayan kungiyar.
Ci gaba da tsarewar da jami’an tsaron Najeriya suka yi wa Kanu, duk da umarnin da kotu ta bayar, cewa an tsare shi a kasar waje ba bisa ka’ida ba, hakan na nufin kungiyar tana gudanar da ayyukanta ba bisa ka’ida ba, kuma ba ta da wani takamaiman tsarin da ya dace.
A madadin hakan, ta karkasu zuwa kungiyoyin mayaka, inda wasu daga ciki ke haddasa rikici da kuma rashin da’a, lamarin da ya haifar wa kungiyar ta IPOB ta rasa goyon bayan da dama daga ’yan kabilar ta Igbo wadanda da farko suka nuna goyon bayansu ga kafuwar ta.
Hare-haren da mayakan suka sha kaddamarwa a shiyyar, wadanda hukumomin tsaron Najeriya suke danganta su da kungiyar, sun yi sanadiyyar hallaka daruruwan fararen hula tun bayan barkewar rikicin a shekarar 2020.
Cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su har da mata da ƙananan yara.
Tsarewar da aka yi wa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ta yi matukar tunzura magoyan bayan kungiyar.
A wani rikici mai muni da ya faru a lokacin hutun Kirsimeti, wani faifan bidiyon wata mata tsirara ya karade kafafen sada zumunta na zamani.
Daga bisani an bayyana ta a matsayin jami’ar sojin Najeriya, wadda ta kai ziyara ga kakarta a jihar Abia, inda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita, inda suka saki bidiyon da ke nuna yadda suke barazanar kashe ta.
Masoyinta, wanda tsohon soji ne, da kuma dan ‘yar uwarta su ma ‘yan bindigar da ke ikirarin ‘yan aware ne sun kashe su.
Wadanda suka yi garkuwa da jami’ar sojin, wadanda suke bayyana kansu a matsayin ‘yan bindiga da ke yaki ga kungiyar ‘yan awaren Biafra, kuma sun nisanta kansu da alaka da kungiyar IPOB.
Wasu shaidun gani da ido sun fada wa mane ma labarai cewa sojoji suna lalata gidaje da wuraren kasuwanci a kauyukan a lokacin da suke neman jami’ar sojin da wadanda suka yi garkuwa da ita.
Kakakin bataliyar sojojin Najeriya ta 34 da ke Obinze a Jihar Imo, Kyaftin Joseph Akubo, ya fada wa mane ma labarai cewa sojojin ne ke da alhakin kaddamar da munanan hare haren.
Sai dai irin wannan lamari ba sabon abu ba ne a yankin.
A wani mummunan lamari irinsa, a watan Oktoba na 2021, al’umma sun zargi sojoji da ƙona gidaje 40 a ƙauyen Izom da ke jihar Imo, bayan da aka kashe sojoji biyu da farar hula ɗaya a wani tashin hankali da aka yi tsakanin sojoji da al’ummar yankin.
Haka nan kuma an zargi masu aikin tsaro na sa-kai da laifin tafka munanan ayyuka.
Ɗaya daga cikin misalan irin haka shi ne kisan da aka yi wa wasu matasa biyar waɗanda aka ce sun fito ne daga wurin wani bikin aure a ƙauyen Awomama,na Jihar Imo a cikin watan Yulin shekarar 2022