BADA KALAR CHANJI KUDI Wasu al umma kasar nan suna kallon kamar almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) dadin abinda ke faruwa a lokacin mulkin nan na Buhari suke yi.




Amma ai bai kamata a manta da cewa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky

 su ma Mutane ne kuma suna rayuwa ne a cikin kasar nan tare da sauran Al umma. Duk abinda kowane Dan kasa yake ji Almajiran Sheikh Zakzaky (h) suna jin sa kuma Babu abin farin ciki da jin dadi ga shigar al ummar musiba ko tsanani na rayuwa.


Dalilan da suka sa wasu suke kallon Yan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Zakzaky daban da sauran Al ummar kasar nan musamman acikin mawuyancin halin da Azzaluman Shugabanin nan suka jefa Al umma a kasar nan.


Harkar Musulunci da Jagora Shekh Zakzaky  suna da manufa kuma manufar nan itace tabbatar da tsarin Addinin Musulunci akwai Cikakken fata da yakini akan cewa tsarin musulunci Shi kadai ne zai dawo da adalci a kasar nan.


Amma sauran Al umma kasa har gobe suna kallon yan siyasa a matsayin mafitarsu duk da sun shafe shekaru fiye da talatin suna jaraba yan siyasar nan amma babu abinda ya sauya sai ma dada lalacewa.


A Gwagwarmayar tabbatar da addinin musulunci da Sheikh Zakzaky yake Jagoranci a Nahiyar Afurka Babu kabilanci na yare ko sabanin Fahimta na akida wannan shine babban dalilin da yasa Sheikh Ibrahim Zakzaky yake fada da Zalunci da azzalumai idan sukayi zalunci ga kowace kabila (yare)  ko fahimta (akida), madamar abin zaluntar mutum ne da Allah ya karrama.


Saidai su al ummar kasar nan har yanzu suna kan fahimtar kabilanci da Sabanin fahimta na iya zama wata babbar hanyar da za a iya zaluntar wani ko wata kuma a goya baya ga azzalumi madamar akwai ban banci.


Misali: Har yanzu akwai Mutanen da yawa a kasar nan da suke kallon Zaluncin da Wannan Gwamnatin Buhari tayiwa Sheikh Zakzaky (h) da almajiransa a 2015 zuwa 2022, a matsayin adalci saboda Sabanin Fahimta.


Har yanzu akwai al ummar da suke kallon Mulkin Jonathan a matsayin mulkin zalunci amma suke kallon mulkin Buhari na Adalci Saboda kabilanci.


Mu kuma Yan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Zakzaky Sai mukayi fada da tsarin mulkin da ya kawo Jonathan da Buhari kuma mukayi alwadai da zaluncin su ga al ummar kasa ga baki daya. To Idan akwai wani dalili da yasa bamu damu da duk wani yanayi da al ummar kasar nan suke ciki ba baiwuce wannan ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post