Ba'a Cutar Da Wani Annabi Kamar Yanda Aka Cutar Da Ni !!!



@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@


Babu Babbar Musiba da Jarrabawa mai wahalar cinyewa kamar a jarrabeka da rawuya cikin maƙiyanka da kake da tabbacin maƙiyinka ne na haƙiƙa , kuma a buƙaci kayi haƙuri ka jure zama dasu tsawon rayuwarka .


Shi yasa jarrabawa da Musibar da aka saukarwa Manzon Allah (saww) suka fi na kowanne abun halitta girma da nauyi , saboda yadda ya rayu da manyan magauta da maƙiyansa da za su cutar dashi har bayan rayuwarsa , amma kuma wasunsu a ko yaushe suna tare dashi . 

Ya zo a Hadisi Annabi (saww) yana cewa : 

Ba'a cutar da wani Annabi kamar yadda aka cutar dani .

Kuma dama ita Musiba da Bala'i ana saukar dasu ne ga mutum Gwargwado Girma da matsayinsa, Gwargwadon Girman Musiba Gwargwadon matsayi da daraja ne , kamar yanda Gwagwadon Aji da matakin mutum a Karatu yake kasancewa gwagwadon Jarrabawarsa .

To in kana so ka ɗan fahimci girma da matsayin jarrabawa da Musibar Annabi (saww) to ka kwatanta ɗan hararo matsayinsa a wurin Allah ya yake ? 

Albusiiri a haƙƙin matsayinsa yana faɗi yana cewa : 


فإن فضلَ رسولِ اللهِ ليسَ لهُ 

حَدٌّ فيُعْرِبَ عنه ناطِقٌ بفَمِ 


لو ناسبتْ قدرهُ آياتهُ عظمًا 

أحيا اسمهُ حينَ يُدعى دارسَ الرِّممِ


 لَمْ يَمْتَحِنَّا بما تعْمل العُقولُ بِهِ 

حِرْصًا علينا فلمْ ولَمْ نَهَمِ


Lallai an jarrabi Manzon Allah (saww) da Maƙiya na ciki da waje (Kafirai da Munafukai) , wasu Allah ya bashi labarin duk abinda za suyi a bayansa , na daga karkashe Zuriyarsa da Ƙoƙarin jirkita Addinin gaskiya da yazo dashi su maida shi Mulki da gado , wasu tun yana raye sun sha ƙoƙarin kasheshi Allah ya kuɓutar dashi .

Wace irin Jarrabawa ce ta wuce ace maka : Wannan da zuriyarsa sune makasanka da Ƴaƴanka da zuriyarta a bayanka amma kayi haƙuri ka jure . 

Lallai ba kamar Manzon Allah (Saww) wajen haƙuri da juriya da dakewa duk dan saboda Addinin Allah da biyayya ga Allah Ta'ala.

Wannan wane irin Haƙuri ne !!!!!

Ya Rasulallahi Mun gode maka da dukkanin Ma'anoni da kalmomin godiya , Allah ya ƙara maka Wasila , fadila da kusanci Gwagwadon Ƙadarinka mai girma .


ABUN TAMBAYA ???


Shin Manzon Allah (saww) yana buƙatar wani sakamako ko lada da zamu saka masa dashi bisa wannan haƙuri , juriya da fama da yasha na tsawon shekaru duk dan saboda mu ???


A'a ! Babu abinda yake nema garemu face tsantsar ƙaunar Makusantansa , da kuma kiyaye haƙƙi da alfarmarsu a bayansa , Allah Ta'ala yana cewa :


قُل لَّا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلَّا الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَىٰ ۗ


Uwa uba mu koma garesu a bayansa , mu riƙesu a matsayin Jagoran Addini da Rayuwarmu har mu riskeshi tare dasu a Tafki , in har munyi hakan na ba za mu taɓe ko mu shiga garari ba har abada , wannan Hadisi ne Ingantacce kuma tabbatacce wurin duk Musulmi sun haɗu akansa , cewa ya bar mana Alkur'ani da iyalan gidansa Tsarkaka babu maimmusun hakan , to ba'a anan gizon je saƙa ba , abun Tambaya anan shine :


Shin an saka masa da wannan abu da ya nema daga garemu haƙiƙanin sakawa ?


Shin an kiyaye amanarsa haƙiƙanin kiyayewa ??


Shin an kula masa dasu an koma garesu dan neman a tsira daga ɓata a bayansa ???


Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


8/Jumadha Thaniniya / 1444H - 1/1/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post