Ba Zaku Gane Maza Security Ba Ne Ga Mata Sai Mijinki Ya Rasu Ko Kun Rabu, Cewar Jamila Ibrahim




Duk ranar da akace baki da Aure to fa sai a hankali kin zama hanya mai insecurity, keda hanyar Zamfara ko Rijana na Kaduna kusan ɗaya.


Yo harda Wanda Bai isa ya maki magana ba zaiyi.


Amma in kina da Aure koda mijinki baya taɓuka maki komai ke kike ciyar dashi mutane ba zasu taɓa miki kallon banza ba.


Don Allah ƴan uwa mata mune zamu gayawa juna gaskiya idan matsalar da kike fuskanta ba matsala ta transformer ba ce da baya kawo wuta, ba kuma dukanki yake ba kiyiwa Allah kiyi haƙuri ki zauna.


Babu Auren da ba'a fuskantar matsala sai dai muce na wani yafi na wani.


Babban matsalar bai wuce talauci ba, kuyi haƙuri lokaci ne, wannan keburan na taba kowa dan dai mutane basu fito sun faɗi matsalarsu ba ne.


Ina bawa duk wata matar Aure haƙuri, a ƙara haƙuri, Allah ya cigaba da baku haƙuri ya biya maku buƙatunku na Alkhairi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post