Ayyamu Sayyada Fatima (s'a) Tsokar Jikin Manzon Allah (S)...!!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]



Ranakun Tunawa da Haihuwar Sayyida Fatima, Ranaku ne na koyon yadda ake gina Ruhu, ake Kawwana Dabi'ah, ake koyon yadda ake yakar Ifiratan Boye dana Bayyana, ake Koyon yadda ake Jihadi da Mujahada domin cimma Fata na Gari, da kuma wargaza Shirin Shedan da Shedanun Mutane.

 Rayuwar Wannan Halitta wadda Saninta da gano Girman Darajarta, ya fi Karfin duk wata Halitta a cikin Mulki take ko Malakuti. Sanin Fatima sai Fadirus Samawati Wal Ardi. A Gangar Jiki ita Mace ce, Macen da ita kadai ce ta fito da Haske 11 wadanda basuda Tamka a cikin Halittun Allah, idan ka cire Mijinta da Mahaifinta.

Darasin farko da za mu iya koya daga Biliyoyin Darasin da ke kunshe cikin Rayuwar Ma'asumah, shine, Idan kana Buri, kana Fatar samun abu, to Zabura domin Cafkarsa.

Fata kadai baya iya fidda Suhe daga Wuta. Batun cewa "Ina fatar komai zai yi dai_dai" ko " Ina Tsammanin Mafarkina zai zama gaskiya". Babu inda zai kaika sai Ramin Rukushi, idan dai bai hadu da Kazar-kazar da Motsi ba.

Fata abu ne mai kyau, amma shi kadai baya Kosarwa. Mayaki na gaske baya da wani zabi a Filin Daga illa cilla Harsasai zuwa ga Makiya. Idan ya ki, ya tsaya fatar ganin bayan Makiyanshi, to shi zai ji nasu Harsashin saman Goshinsa.

Mafi yawan Lokuta cikin Yaki muke, amma bama iya ganewa. A kulkum akwai wasu miyagun Akidu, ko Bakaken Al-adu, ko Batattun Dabi'u dake boye suke yakarmu, suke kokarin kaimu Kasa, ta hanyar amfani da Mutanenda ke kewaye damu.

Sayyida Fatima Makaranta ce Mai Motsi, ka koyamana cewa ba'a yakar Boyayyun Shedanu da Makaman Bayyane kawai. Makaman Badini ake sakawa a tadasu Aiki. Yakin Ruwan sanyi sai Makamin Ruwan Sanyi, Yakin Zahiri sai da Makamin Zahiri.

Idan kana Fatan ganin Al-umma ta gyaru, to tashi za ka yi ka yaki Zalunci. Idan kana Burin gani Kasa ta ci gaba to zabura za ka yi wajen aiki Tukuru a kan tabbatuwar haka. Idan kana Kwadayin neman Ilimi to zare dantse wajen Leka Zauruka da Soraye da Tsangayoyi da Jami'o'i. Idan kana fatan samun Dukiya to babu kai ba bu zama a Dandali, ko Majalisa ko Lungu ko kwana ko Sakon Shiyarku ko Unguwarku ko Gidanku. Dole Ka zabura ka bazama ka je nema.

Kamar yadda ba'a iya Motsi sai idan akwai Fata, hakanan ba'a samun abu da Fata kadai, dole sai an hadashi da Himma da Zabura, da aiki Tukuru kafin cimma Buri.


Shamsudeen Hassan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post