Arewa ma so gabas ita ce yankin da ta kunshi jihohin Adamawa, Borno, Bauchi, Gome, Yobe da Taraba, kuma kowa ya sani cewa wannan yanki ya fi kowanne yanki filayen noma a kasar nan, amma babu filin jirgin jigilar kaya ko guda daya a dukkan wannan yanki.




Dalilin dukkan kayan gona da ake nomawa a wannan yanki shine ma fi yawan kayan da ake jibgewa a Kasuwar dawanau ta jihar Kano. Wato mu muna wahalar noma Kanawa suna sayewa su saidawa turawa da tsada. A bar mu cikin talauci kuma ana magana gadara ana mana dariya.


Hikmar Gomna Mai Mala Buni ita ce ceto wannan yanki na mu na Arewa maso gabas daga wannan yanayin, ta hanyar gina mana Airport na Jigilar kaya, ta yadda manoman mu za su daina saida kayan su araha bulbs a Dawanau, kuma su samu aikin yi, da kudaden shiga.


Da kammala wannan Airport din, yanzu dukkan dan Northeeast zai iya alfahari da cewa shi ma yankin shi ya fara farfadowa, kuma zai iya gogayya da kowanne yanki na kasar nan akan abunda ya shafi tattalin arziki. Dukkan alamu na nuna cewa yan Kasuwar Dawanau dole su yi Hijra su koma Yobe in har suna son saidawa Turawa kaya. Tunda dama chan yawancin kayan mu muke nomawa.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post