Labarin da ke shigo mana yanzu na cewa wasu fusatattun matasa sun jefi Ɗan takarar Gwamnan jihar na jam'iyyar APC Dr. Dikko Umar Radda tare da yi mashi ihun bamayi-bamaso a daidai lokacin da tawagar tashi ta isa garin Ɗanmarke dake ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina
A rahoton da muka samu bayan zantawa da ɗaya daga cikin matasan garin ya bayyana cewa tawagar Ɗan takarar ne suka fara yayyaga allunan siyasar Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke wannan ne dalilin da ya harzuƙa matasan garin.
Haka zalika matasan garin sun fito ƙwansu da ƙwarkwata a saman tinuna suna ƙona tsintsiya tare da ihun bamayi.
Majiya: Blue Print
Tags:
Labarin duniya