Zainabiyyun sun gudanar da taron tunawa da haihuwar Sayyida Zainab (A.s) a Birnin Kebbi. An gudanar da taron ne tsawon kwanaki biyu jere da jere, Alhamis 22 zuwa Jumu'a 23 ga Disambar 2022.
A ranar farko, da misalin 10 na safe, an fara program din da karatun Al-Qur'ani mai girma, sai addu'oi ga Shahidan Zainabiyyun da sauran Shuhadan Harka, bayan kammalawa, sai ziyarar asibiti wacce a ka kai a asibitin 'Sir Yahayya Memorial Hospital' tare da raba kyautukka ga jajirai don murnar da ranar haihuwar Sayyida Zainab (a.s), inda majalisi ya biyo baya, wanda Malam Shamsu Fudiyya ya gabatar.
A rana ta biyu, ranar Juma'a 23rd December, 2022 wacce ita ce ranar qarshe, an fara taron 10:00 na safe Malam Nuriyya Gwandu ce ta fara buɗe taro da addu'a sai karatun Al-Qur'ani da Ziyarar Sayyida Zainab (a.s) wanda Sister Zahra'u Abdulnasir Nepa ta gabatar, Sister Siddiqa Sani ce ta gabatar da jawabin maraba da baqi, daga baya ta sake karanto muqala wato "Paper Presentation".bayan nan sai aka gudanar da muhawara (debate) inda daga bisani babban baqon Malam Shamsu Fudiyya ya sake qawata muhallin taron karo na biyu da gwala-gwalan baitoci ga Sayyida Zainab (a.s).
Malam Halilu Umar ne ya gabatar Jawabi kan 'Muhimman ilimin sister 'yar gwagwarmaya', a cikin jawabin, ya ja hankalin sauran matasa kan muhimmancin neman ilimi. Daga karshe an yanka cake, sister Naqiyya Umar Bello ta rufe taro da addu'a.
#MauludinSayyidaZainab(AS)1444AH