“A jihar Nassarawa, yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka sace ɗalibai ƴan makaranta.”
“A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba suka kai hari makarantar firamare ta karamar hukumar Alwaza da ke karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa inda suka yi awon gaba da dalibai da dama a yankin.”
“Masu garkuwa da mutanen da suka yi awon gaba da daliban firamare da ba a tantance adadinsu ba, an ce sun kewaye makarantar ne a lokacin da yaran ke zuwa makaranta.”
Ba'a dai bayyana inda daliban makarantar suke ba har zuwa lokacin da ake cike wannan rahoto.
“Yanzu haka dai ‘yan sanda sun tabbatar da rahoton, kamar yadda Jaridar ALFIJIR HAUSA ta tabbatar da Hakan.”