[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
Daga Wakilinmu.
Ana zargin jami'an Ƴansanda da buɗe wuta ga Masu kiɗin DJ wanda hajan ya yi sanadiyyar Mutuwar yara biyu a Unguwar Tudun Matawalle cikin Birnin Katsina.
Da Yammacin ranar Lahadi 1 ga Janairun 2023, a Unguwar Tudun Matawalle da ke cikin Birnin Katsina, jami'an 'Yansanda suka far wa masu shagalin biki wanda ya yi sanadiyar rasa wasu yara 'yan ƙasa da shekaru goma a wajen Kiɗan.
Kamar yanda ɗaya daga cikin Iyayen yaran da abin ya shafa, ya bayyanawa Jaridar Katsina City News, "Jami'an na 'Yansanda sun shiga Unguwar inda suka iske ana kiɗan DJ don gudanar da Biki, bisa Al'ada cewa a garin Katsina idan ana wata sabga a kan ɗauko masu kiɗan DJ don murna da shagalin bikin." In ji shi.
Ya ce, 'Yansandan sun shiga Unguwar inda suka ce wa Matasan da ke kidan da su tashi su bar wajen, amma suka ƙi su tashi, sakamakon haka ne 'Yansandan suka buɗe wuta kan mai-uwa-da-wabi, inda lamarin ya rutsa da wasu yara da suka taso daga Islamiyya zuwa gida.
Majiyar ta ci gaba shedawa Jaridunmu cewar, Yara biyu da suka mutu sakamakon harbin harsashi, ba su gaza shekaru goma ba, inda mutum uku suka jikkata suna kwance a Asibiti a halin yanzu.
Malam Musa Ali, malami ne na makarantar Islamiyya wanda ya rasa ɗalibinsa guda ɗaya, ya bayyana ma Jaridunmu cewa; "Ɗalibin namu mai shekaru tara ya zo makarantar yamma har ma an biya masa Allonsa ya wanke an masa wani sabon rubutu, bayan an tashi a kan hanyarsa ta zuwa gida abin ya rutsa da shi. In ji shi.
Ya kara da cewa, "Ba mu ma san halin da ake ciki ba, sai washe gari mahaifiyar yaron ta zo makarantar take cewa ai kuwa yaron nan ga abin da ya same shi; har ma Allah ya yi masa rasuwa."
Don jin ta bakin hukumar 'yansanda, mun aika sako amma har zuwa haɗa wannan rahoto ba mu samu amsa daga gare su ba.