Akwai bukatar akalar rubuce rubucenmu ya koma kan Munasabar Haihuwar Shugabar Matan Talikai, Sayyida Fatima Azzahra (SA), wacce aka haifa a ranar 20 ga Jimadal Thani.....!!




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 




Bisa Ittifakin kowa, Sayyida Zahra (SA) ce kadai 'Yar da Annabi (S) ya bari. Kuma ta wajenta ita kadai ne aka gaji Manzon Allah (S), ita kadai ce tsatson Manzon Allah (S) ya wanzu ta wajenta. Don haka ta isa kowane irin girman matsayi da daraja.


Akwai bukatar a sanar da al'umma ko wace ce Sayyida Zahra, a sanar da su rayuwarta da darajojinta da kuma irin tafarkinta na riko da addini da tsayuwa a kan gwagwarmayar wanzar da hakikarsa, da iliminta da halayenta na kirki irin su kyauta, hakuri da afuwa, ibada da soyayyarta da duk hali na kwarai abin koyi.


Mu yi kokarin ganin mun shagaltu da wadannan, mu runtse idanunmu daga yaran Jahiliyya da ba su da aiki sai haifar da kace-nace a cikinmu da baci ko aibata juna da soke-soke din nan da za ka rasa wa yake amfana da yada sharruka da hujumi da fitar da juna daga Da'irar Harka Islamiyya.


Allah Ya sada mu da ceton Sayyida Zahra (SA) 🌹

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post