Ko kun san a jiya Lahadi 1 ga watan Janairun 2023, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da membobin Technology Forum na Harkar Musulunci a gidansa dake Abuja.
Membobin sun yi amfani da wannan dama wajen gabatar da ayyukansu tare da ayyukan da suke a kai ciki harda wannan shafi na Kundin Tarihin Harka da abubuwan da ya kunsa, da yadda muke son ya kasance.
Su Malam (H) sun bayar da shawarwari da goyon baya da kuma yadda yakamata ayyukan su kasance.
Alhamdulillah ziyara ce da itama ta shiga KUNDIN TARIHIN HARKA.
Hotuna: @Szakzakyoffice
01/01/2023
©KUNDIN TARIHIN HARKA
Ta ya za ku riski KUNDIN TARIHIN HARKA kafin kaddamarwa?