Aikin jarida a Mahangar addini musulunci kashi na biyu.




 Aikin jarida a Mahangar musulunci; aikin Jarida na wannan zamani yanada banbance-banbance da saɓani da na addini musulunci. Misali kowa yasan Hadisin nan na Bukhari da Muslim na An-Nawawiy na 15 wanda yai bayanin cewar “ Duk wanda yai amanna da Allah da ranar ƙarshe, ya faɗi alheri ko ya yi shiru.


MAGANAR MUSULUNCI: haka kuma a cikin Alqur'ani mai girma Surah, Al-Ahzab Q33:70 ''yaku wadanda kukayi imani, kuji tsoron Allah kuma ku faɗi kalmomin da suka dace''. Kuma ku faɗi ga Mutane kalmomin na gari Surah Al-Baƙarah Q2:84 


Aikin jarida ya samo asali ne bayan juyin juya hali wato “ Industrial Revolution” ( 1760 - 1840 ) da akayi a turai wanda ya haifar da abin da ake ma laƙabi da, 'mass society '. Al'umma bila'adadin na aiki a masana'antu, kuma suna buƙatar wani abu da zai ɗauke musu kewa a wurin aiki. Ta haka ne aka fara wallafa takardu masu kama da jaridu ana rabawa ko siyasarwa ga ma'aikata domin su nishaɗanta yayin  aiki.


TAƘAITACCEN TARIHI:  su dai waɗannan jaridu ƙanana ne, kuma sukan ƙunshi labarurruka na unguwanni da garurruwa, da labari aure da biki da makamantansu. Aikin jarida na taka rawa yazo da tsari, ƙa'idoji da tsarabe-tsarabe wanda yasa ya ɗora ya kawo iyanzu. Waɗannan sun haɗa da, da ƙa'idojin ɗauko labari ( News velues ) Dokokin gudanar da aiki ( Code of ethics ).


ƘA'IDOJIN ƊAUKO LABARI: 


HUMAN INTEREST ( labari ya zamo abin sha'awa)


 ACCURACY ( Labari ya kasance gaskiya, ba ƙirƙira ba ).


TIMELINESS ( Labari ya kasance sabo, ba kwantai ba). 


PROXIMITY (  labari ya kusanci masu amfana );


UNUSUAL / ODDITY ( abin al'ajab, mutum ya ciji kare );


DOKOKIN GUDANAR DA AIKIN ( CODE OF ETHICS ) 


• Ba da cin hanci ( reward and gratification ).

• Kariya da rashin bayyana sirri.

• Tattaro labari.

• Bayanin sirri na mutum. 

• Kaucewa cin zarafi.

• Satar aiki .

• Haɗa kan al'umma ( Public interest )

• Copyright ( satar aiki domin neman kuɗi ).

• Baiwa 'yan jarida 'yancinsu.

• Bin ƙa'idar aiki. 

• Nuna ban-banci. 

• Kariya ga yara da ƙananan ƙabilu.

• Gaskiya da adalci.

• 'Yancin faɗar albarkacin baki.


ƘORAFE-ƘORAFE AKAN AIKIN JARIDA:  Mutane da dama na ƙorafi bisa yadda 'yan jaridu kan gudanar da ayyukansu. Haka kuma, mutane da dama sunyi wa aikin mummunar fahimta. Yawancina 'yan jaridu sun ba da gudunmawa wajen wannan mummunar fahimta sabili da yadda sukan gudanar da aikin wanda ya ƙunshi son zuciya.


ƘORAFE-ƘORAFE: iren-iren ƙorafe-ƙorafe da al'umma kanyi ga 'yan jaridu sun haɗa da;


• Yin ƙazafi.

• Yin ɓatanci.

• Haɗa husuma.

• Cin zarafi.

• Yin ƙarya .

• Yin sharri, da makamantansu.


Insha Âlláh zamu haɗu a kashi na uku domin cigaba daga inda na tsaya cikin rubutu aikin Jarida a Mahangar addini musulunci.


__faruq Sani Kudan ( Abban Jeedderh )

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post