Abubuwan da mukeyi na shangiya da saɓo ba Inyass ne ya koya mana ba - Ɗan-Anti.




Fitaccen jagoran masu halatta haram a addinin Musulunci Ɗan Anti, bisani masu kirayen junansu da Allloli, Hakazalika masu ikirarin su ne ainihin mabiya ɗariƙar Tijjaniya ya bayyana cewar abubuwan da suke na mai da Halitta Allah, halatta shan giya da zina ba ɗarikar Tijjaniyya da faydar Shehu Ibrahim Niass ne su koya masu ba"  


Ɗan-anti ya bayyana hakan ne bayan wani zaman 'yar ƙure da malamin ɗarikar Tijjaniyya yayi dashi mai suna Sheikh Aminu Under Seventeen,  a shafin fitaccen ɗan jaridar nan mai suna Sarki Zaaki Mkk.  


"A kwanakin baya ne dai ɗan Anti ya bayyana cewar malaman ɗarikar Tijjaniyya tsoron sa suke cikin wata hira da yayi a wani gidan rediyon yanar gizo na mabiya ƙungiyar Izala mai suna ISHA FM, sai dai jiya bayan ya zauna da malamin Tijjaniyya ya bayyana cewar duka abubuwan da suke yi ba Shehu Inyas da ɗarika ne su koya masu ba."

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post