ABIN TAUSAYI: Yadda Wasu Almajirai Ke Kwana A Waje Cikin Wannan Muku-mukun Sanyin A Birnin Kebbi




Wannan hotunan da kuke gani, hoton wata Makarantar Almajirai ce dake unguwar Rafin Atiku a nan Birnin Kebbi dake jihar Kebbi.


Abinda zai baku tausayi shine na ɗauki wannan hoton ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare, kuma cikin wannan sanyin da ake kwadawa, amma wasu daga cikinsu basu da hatta ƙyallen rufe jikinsu.


Ballantana a yi maganar ɗakin da za su shiga su ɓuya, domin ba su da shi.


Abin haushi da takaicin kuma a nan shine, duk wannan yanayin da yaran nan suke ciki iyayensu fa ba su taimakonsu da komai. Hasali ma suna can ƙauye suna jiran yaran su zo da wani abu idan za su koma gida lokacin damina.


Menene ra'yinku akan wannan al'amari?



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post