[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]
A Rana Mai Kamar Ta Yau 17 Ga Watan Janairun 1983, Shugaban Najeriya na lokacin, Alhaji Shehu Shagari, ya gudanar da taron manema labarai inda ya umurci dukkan bakin haure (mafi yawansu 'yan Ghana) da ba su da takardun da suka dace da su fice daga kasar nan da 'Yan makonni.
Yawancin 'yan Ghana sun yi gaggawar tattara kayansu a cikin wata katuwar jakar Buhun Leda mai ratsin ja da shudi, da haka aka Sami Sunan fitacciyar jakar "Ghana must go".
Fitar da 'yan Yammacin Afirka daga Nijeriya Ya faru bayan umarnin zartarwa a 1983 daga Shugaban Najeriya Shehu Aliyu Shagari wanda aka tilasta wa baƙi su bar kasar Sakamakon na odar Shagari, sama da Yan kasashen Afirka Ta Yamma miliyan biyu aka kora" ciki har da 'yan kasar Ghana miliyan Daya
Jama’ar Kasar Ghana mazauna Najeriya a shekara 1983 wanda yawan su ya kai mutum Miliyan daya, Najeriya tayi zargin cewa yawancin bakin haure ne. Kuma A Lokacin Ba'a jima Da Gama Rikicin Maitsine Ba! Gwamnatin Najeriya Tayi Zargin Da Akwai Yan Kasashen Yammacin Afirka A Cikin Almajiran Maitatsine Da Su ka Tayar Da Tarzoma A Kano A Shekarar 1981. Wannan hukunci da kasar Najeriya ta dauka ya girgiza duniya.
Yan Najeriya sun yi murna matuka lokacin da aka sanar da wannan da korar, su kuwa yan Ghana Wannan bacin rai ne da ba zasu taba mantawa ba.
A Ranar 10 Ga Watan Mayu Na Shekarar 1983, Gwamnatin Najeriya ta Fitar da Sanarwa Ko dai Yan Ghana Su Fice Daga Kasar Ko su Fuskanci Kamu Da Gabatar Dasu A Gaban Kotu Da Shan Dauri.
A Najeriya an rika cika manyan Motoci da Jiragen ruwan daukar kaya da yan Ghana, sa’annan aka sanya Sojoji da su sa ido, su tabbatar kowannen su ya bar Najeriya.
Yawancin Yan Ghana sun tafi sun bar Kadarori da Arzikin su saboda rashin samun takardun zama daga Gwamnatin Najeriya.
Gwamnatin kasar Ghana ta wannan lokacin tayi tofin Allah tsine da nuna bacin rai Tace “Najeriya ta ji kunya.
Wannan mataki da Najeriya ta dauka ya saba da tsarin kungiyar hadin kan kasashen Afirka” Ta OAU, nan da nan Kalmar ‘Ghana must go’ ya zama abin raha tsakanin yan Najeriya, suna ganin Gwamnatin Shagari tayi abin daya kamata. Sun sa ran cewa korar mutanen Ghana daga Najeriya zai kawo samun aikin yi.
IDAN ZA'AYI TAFIYA DOLE A NEMI JAKA.
Wannan Dalili Ne Ya Sanya, "Yan Ghana Nemo Manyan Jakukkuna Domin Zuba Kayayyakinsu.
Daga Nan A ka Sanyawa Jakukkunan Da Kuke Gani A Yau GHANA MUST GO.
Tafiyar yan Ghana baisa Najeiya ta zama wata madaukakiyar kasa ba kamar yadda ake zato, sai dai ma yan Najeriya sun gano wasu gaggan matsaloli ne wadanda ma sun fi karfin batun mamaye ayyuka da ake cewa yan Ghana sun yi.
Ya zamto yan Najeriya basa iya yin Ire-iren kananun ayyukan da yan Ghana ke yi a baya, saboda basu saba da ayyukan ba, sa’annan kuma wasu daga cikin Yan Ganan suna Aiki A kananan masana’antu ne, inda tafiyarsu ta jawo kullewar ire iren masana’antun, kuma Gwamnatin Najeriya bata yi wani yunkurin farfado da su ba.
Har karshen 1983, kasar Najeriya bata samu wani canjin Azo a gani ba, yan Najeriya na cewa Gara jiya Da Yau.
Daga nan ne aka fara tunanin cewa akwai babbar matsalar dake damun tattalin Arzikin kasar.
A ranar 31 ga watan Disamba 1983 Janar Muhammadu Buhari ya kwace mulki, inda ya jingina hujjarsa ta yin haka ga Almundaha, da cin hanci da rashawa, Da Tsadar Kayan Masarufi, Da Rashin Magani A Asibiti, Da Rashin Ayyukan Yi A Tsakanin Matasa, Da Yawan Daukewar Wutar Lantarki, dake Gudana a Karkashin Gwamnatin Shehu Shagari.