Zuma Rock, A Jihar Neja Da Ke Tarayyar Najeriya.!!!

 



@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@


Dutsen Zuma, wani babban dutse ne, wadda ke a cikin Ƙaramar Hukumar Suleja, a jihar Neja da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya. 


Har ila yau, Dutsen ya kasance a yammacin Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar. 


Watau, ya na kan babbar titin Abuja zuwa Kaduna, daga garin Madalla. 


Ya na da tsayi kimanin mita 300 (980ft) sama da kewayensa, fiye da matakin teku. 


Dutsen Zuma, ya na da tsayi sosai, domin ya fi gidan NECOM da tsayi sau Huɗu (mafi tsayin gini a jihar Legas, a 1979), kuma ya fi dutsen Aso (Aso Rock) da dutsen Olumo (Olumo Rock) gaba ɗaya.


Bugu da ƙari, dutsen ya na ɗaya daga cikin mafi girma a duniya. 


Ƴan ƙabilar Zuba na jihar Neja ne suka gano dutsen a ƙarni na 15, waɗanda suka kira shi da "Zumwa" (a place of Guinea fowls) saboda yawaitar tsuntsayen Guinea da suke wurin a wancan lokacin. 


Mutanen ƙabilar Gwari (Gbagyi) ne suka yi amfani da shi a matsayin kariya a lokacin yaƙoƙi. 


Dutsen ya na da wasu ababe waɗanda ba kasafai ake gani ba, yakan nuna wasu sassan halittar jikin ɗan Adam kamar; Fasalin fuska, Baki, Hanci, da Idanu. 


Sannan a ƙarƙashin dutsen, akwai ruwa da yake ɓuɓɓugowa wadda yake isa zuwa wasu gonaki na maƙwafta, kuma masu Yawon Buɗe Ido kan ziyarci wurin daga sassa daban-daban na ƙasar. 


Tafiya zuwa saman dutsen ya na ɗaukar kimanin sa'o'i biyar. 


Ya kasance ɗaya daga cikin fitattun wuraren tarihi a Najeriya, kuma tun shekara ta 1999 ake buga takardun kuɗin ƙasar na Naira 100 kawo yanzu.


Abubakar SD

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post